✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun saki Sakataren Tsare-tsaren APC da suka sace a Kaduna

A ranar Juma’ar da ta gabata ne suka sace shi a gidansa da daddare

Mutanen da suka sace tsohon Sakataren Tsare-tsare na jam’iyyar APC a Jihar Kaduna, Alhaji Kawu Ibrahim Yakasai sun sako shi da yammacin Lahadi.

Yakasai, wanda kuma tsohon Shugaban Karamar Hukumar Soba ne kuma tsohon dan majalisar ne da ya wakilci yankin.

Jami’in hulda da jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Jihar, DSP Mansir Hassan, ne ya tabbatar da sakin dan siyasar a zantawar shi da wakilin mu ta wayar salula.

An sace Alhaji Kawu Ibrahim Yakasai ne a ranar Juma’ar da ta gabata lokacin da wasu da ake zargin mahara ne suka shiga har gidan shi da misalin karfe 9:00 na dare suka yi awon gaba da shi.

Binciken Aminiya ya gano cewa, akwai kaninsa Yakasai da ke hannun ’yan bindiga fiye da shekara guda kuma har yanzu babu ko labarin shi.

Har ila yau, kimanin mako uku da suka gabata, ’yan bindigar sun sace wani jagoran jam’iyyar APC, Alhaji Sabitu Ahmed a gundumar Garu da ke wannan Karamar Hukuma ta Soba.

%d bloggers like this: