✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi jana’izar mamatan da hatsarin kwale-kwala ya kashe a Neja

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 10 na safiyar ranar Lahadi.

An yi jana’izar mamatan da hatsarin kwale-kwale ya rutsa da su a Jihar Neja.

Aminiya ta ruwaito cewa aƙalla mutum 24 galibinsu manoma ne suka mutu, yayin da wasu da dama suka ɓace a lokacin da wani kwale-kwale ɗauke da fasinjoji ya kife a garin Gbajibo, a Karamar Hukumar Mokwa da ke Jihar Neja.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 10 na safiyar ranar Lahadi.

Rahotonni na cewa fasinjojin kwale-kwalen sun fito ne daga garuruwan Gbajibo da Ekwa da Yankeiade.

Wakilinmu ya ambato Shugaban Karamar Hukumar Mokwa, Jibrin Abdullahi Muregi na cewa an tsamo gawarwaki 21.

Jami’an hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar sun tabbatar da faruwar lamarin, inda suka ce suna tattara alƙaluma domin sanin haƙiƙanin adadin mutanen da lamarin ya shafa.

Hatsarin na zuwa ne kwana biyu bayan da wani kwale-kwale ya kife ɗauke da fasinjoji ciki har da mata da ƙananan yara a birnin Yola na Jihar Adamawa, lamarin da ya haddasa asarar rayuka.