✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan Bindiga Sun Kashe Gomman ’Yan Banga A Neja

An bayyana damuwarsa kan yadda matsalar tsaro ke kara kunno kai daf da lokacin da ake shirin fara noman damina.

Gomman ’yan banga ne suka gamu da ajalinsu a hannun ’yan bindiga a yankin Dogon-dawa da ke Ƙaramar Hukumar Mariga a Jihar Neja.

’Yan bangan da ake kira ’yan sa-kai a yankin sun rasa rayukansu ne bayan wani mummunan arangama da ya rutsa da su a Dogon-dawa da ke jihar.

Bayanai sun ce ’yan sa-kan sun faɗa komar ’yan bindigar a hanyarsu ta zuwa maboyarsu da ke wani daji a yankin.

Aminiya ta ruwaito Shugaban Ƙaramar Hukumar Mariga, Abbas Kasuwar Garba yana tabbatar da faruwar lamarin.

Ya bayyana abin da ya faru a matsayin abin ta da hankali da rikitarwa.

Shugaban ya ce, ba iya ’yan sa-kai aka kashe ba, su ma ’yan ta’addar an ragargajesu, amma kawo yanzu ba a san adadin waɗanda aka kashe ba.

Ya bayyana damuwarsa kan yadda al’amarin rashin tsaro ke kara kunno kai daf da lokacin da ake shirin fara noman damina.

“Kafin yanzu, hankali ya fara kwanciya a yankinmu, muna murna jama’armu za su yi noma cikin aminci, ba kamar shekarar da ta gabata ba, da aka hana su noma ba.

“Faruwar wannan lamari ya mayar da hannun agogo baya ne, domin a yanzu da ake shirin shiga daji domin fara noman damina, wannan ba abun wasa bane, muna fata gwamnati za ta ɗauki matakan da suka dace.”

Ya kara da cewa yana jajanta wa jama’a kuma yana fata kowa zai kwantar da hankalinsa ya natsu.

Sai dai da Aminiya ta tuntubi Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya ce “wannan harin ba a Jihar Neja ya faru ba.”