Aƙalla jami’an tsaro shida ne suka rasu bayan wata arangama da suka yi da ’yan bindiga a yankin Gada Woro a kan hanyar Patigi da ke Ƙaramar Hukumar Edu a Jihar Kwara.
Waɗanda suka rasu sun haɗa da ’yan banga guda biyar da ɗan sanda ɗaya.
- ‘Mutum 600 da suka bace a ambaliyar Mokwa sun mutu’
- Lakurawa sun kashe mutum 15 a harin ramuwar gayya a Sakkwato
Wasu sojoji biyu, ’yan sanda biyu sun samu raunin harbin bindiga a fafatawar da ta faru a ranar Litinin.
Waɗanda suka rasu sun haɗa da Mohammed Nma Dsuru daga Kokodo, Yanda daga Lafiagi, da Ndagi Saraka daga Edogi.
Rahotanni sun ce ’yan bindigar da yawansu ya kai ɗaruruwa sun kai wa tawagar jami’an tsaro farmaki a cikin daji, inda aka yi ta musayar wuta.
Wasu daga cikin waɗanda suka jikkata an kai su Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ilorin (UITH) domin samun kulawa.
Wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta ya nuna yadda aka fafata a dajin.
Wasu mazauna yankin sun ce lamarin ya fara ne a ranar Asabar, lokacin da aka sace wani fitaccen mai sayar da magungunan gona wanda ya dawo daga aikin Hajji.
’Yan bindigar sun shigo da babura, suka shiga gidansa da ke unguwar Taiwo da misalin ƙarfe 1 na dare sannan suka tafi da shi.
A ranar Lahadi, sun sake kai wani hari inda suka sace ɗan kasuwa mai sana’ar POS, Alhaji Yaman da wani mutum mai suna Usman.
’Yan banga sun samu nasarar ceto mutum ɗaya daga cikinsu.
Wasu daga cikin al’ummar yankin na zargin cewa wasu mazauna garin na taimaka wa ’yan bindigar a ɓoye, duba da cewa yawancin waɗanda aka sace matasa ne kuma fitattun ’yan kasuwa a yankin.
An yi ƙoƙarin jin ta bakin kakakin ’yan sandan jihar, Adetoun Ejire Adeyemi, amma ba ta ɗauki waya ko amsa saƙon da aka aike mata ba.