Babbar Kotun Jihar Filato da ke zamanta a Jos, ta yanke wa dalibin nan na makarantar GSTC Bukuru, Odey Emmanuel, hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda kashe malamin makarantarsu a kan abinci.
Alkalin kotun, Mai Shari’a S.J. Bakfur, ya ce an sami Odey ne da laifin na kisan kai wanda kotun ta ce ya saba da tanade-tanaden sassa na 188 na 189 na kundin dokar manyan laifuffuka ta jihar Filato ta shekara ta 2017.
- Za a fara cin tarar masu shigar banza N50,000 a Delta
- Ko ɗaya Buhari bai yi wa takarar Tinubu zagon ƙasa ba – Garba Shehu
A cewar alkalin, masu shigar da kara sun gabatar da hujjojin da suka iya gamsar da kotun cewa wanda ake zargin ya aikata laifin da aka zarge shi da aikatawa.
Babban lauyan gwamnatin jihar kuma Kwamishinan Shari’a, Philemon Audu Daffi ne ya jagoranci lauyoyi masu gabatar da kara.
Lamarin dai ya faru ne ranar 30 ga watan Yulin 2022, a cikin harabar makarantar da ke karamar hukumar Jos ta Kudu.
Lauyoyin sun shaida wa kotun cewa dalibin ya kasha malamin ne mai suna Job Dashe a dakin girkin makarantyar lokacin da ake rabon abinci ga dalibai.
Sun ce a lokacin ne malamin a hukunta dalibin bisa zargin ya karbi kason abinci har sau biyu, inda dalibai suka tabbatar da haka, lamarin da ya harzuka dalibin.
Daga nan ne dalibin ya dauko wuka ya daba wa malamin a kahon zuciya, nan take aka garzaya da shi asibiti amma kafin a je y ace ga garinku nan.
Sai dai ko da a aka karanta masa laifin da aka zarge shi da aikatawa a kotun, dalibin bai musa ba.
Da yake yanke hukuncin, Alkalin kotun ya jaddada cewa kisan malami a makaranta babbar barazana ce ga al’umma da ya zama wajibi a dauki tsattsauran mataki a kai.