Al’ummar Ƙaramar Hukumar Isa da ke Jihar Sakkwato, sun roƙi gwamnatin jihar da ta Tarayya da jami’an tsaro da su kai musu ɗauki kan barazanar da ƙasurgumin ɗan bindiga Bello Turji ke musu.
A farkon makon nan ne aka samu labarin cewa Bello Turji ya bai wa mazauna wasu yankuna a Isa wa’adin gina masa ƙaramin dam ko kuma su fuskanci hukunci mai tsanani.
- Babu wanda zai manta da gudunmawar da Wike ya ba ni — Fubara
- An samu amincewar yi wa Dantata jana’iza a Madina
Har ila yau, ya umarce su da su bar garuruwansu, domin ba ya buƙatar ganinsu a wajen.
Wani mazaunin yankin, Wanzami Abubakar Isa, ya bayyana damuwarsa cewa suna zaune garuruwansu kamar baƙi.
“Abin takaici ne yadda ’yan bindiga ke ba mu umarni a garinmu na haihuwa. Muna roƙon gwamnati ta taimake mu.“
Shi ma Alhaji Abdullahi Isa ya ce, “Rayuwarmu ta shiga mawuyacin hali. Ba za mu iya ci gaba da rayuwa a haka ba.
“Ta yaya za mu bar gidajenmu saboda barazanar ɗan bindiga? Gwamnati ta yi wani abu cikin gaggawa.”
Wani mazaunin yankin, Bashar Ahmad, ya ce ba daidai ba ne a bar Turji yake cin karensa babu babbaka.
“Gwamnati ta kare mu, mu ma ’yan ƙasa ne kuma muna da ’yancin zama lafiya.”
Sai dai duk ƙoƙarin jin ta bakin Shugaban Ƙaramar Hukumar Isa, Alhaji Sharifu Kamarawa, da mai bai wa gwamna shawara kan harkar tsaro, Ahmad Usman, bai yi nasara ba, domin ba su amsa kira ko saƙon da aka aike musu ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.
Yanzu haka, ko da yake Turji bai bayyana ranar da zai kai hari ba, akwai fargaba sosai a yankin.
Jama’a na ganin ya kamata gwamnati ta ɗauki mataki mai tsauri, maimakon ci gaba da yin sulhu da ’yan bindigar da ke addabar yankin gabashin Sakkwato.