✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fararen hulan Isra’ila sun kai wa sojojin ƙasarsu hari

fararen hula ’yan Isra'ila sun yi wa sojojin ƙasarsu ruwan duwatsu a Yammacin Kogin Jordan

Rundunar sojin Isra’ila ta tabbatar da wani hari da fararen hula’yan ’yan ƙasar suka kai wa sojojinta.

An kai wa dakarun rundunar sojojin ko-ta-kwana na Isra’ila hari ne a yankin Gaɓar Yammacin Kogin Jordan.

Yahudawa ’yan share wuri zauna suka kai wa sojojin na Isra’ila harin ne a yayin da sojojin ke aiwatar da wani samamen tare da yin kame a yankin, mai suna Kafr Malek.

Sanarwar da rundunar ta fitar ta ce, “fararen hula ’yan Isra’ila sun yi wa jami’an ruwan duwatsu tare da cin zarafin sojojin ta jiki da ta baki, ciki har da kwamandan rundunar.”

Ta kara da cewa fararen hular sun yi ɓarna tare da lalata motocin sojoji, har ma sun yi yunkurin bige jami’an tsaro.

Rundunar ta bayyana cewa lamarin ya faru ne a yayin da fararen hula’yan Isra’ila ke tuƙi zuwa wani wuri da aka ayyana a matsayin wurin da sojoji suka kulle.

Sanarwar ta ce jami’an tsaro sun tarwatsa taron, kuma an kama mutum shida tare da mika su ga ’yan sandan Isra’ila don ci gaba da bincike.