✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka yi jana’izar kwamandojin Iran da Isra’ila ta kashe

A safiyar Asabar daruruwan dubban mutane ne suka fito ɗauke da tutocin ƙasar suna wake-waken jinjina domin karrama kwamandojin da suka kwanta dama a wurin…

Iran ta gudanar da gagarumin jana’izar tare da karramawq ga kwamandojinta da masana kimiyyar nukiliya da wasu ’yan kasar da Isra’ila ta kashe a yankin kwana 12 da aka gwabza a tsakanin ƙasashen.

Iran ta shirya gagarumin jana’izar a ƙwaryar birnin Tehran kwana huɗu bayan Isra’ila ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta a yaƙin da ɓangarorin biyu ke iƙirarin nasara a yaƙin da aka fara ranar 13 ga Yuni, 2025.

A safiyar Asabar daruruwan dubban mutane ne suka fito ɗauke da tutocin ƙasar suna wake-waken jinjina domin karrama kwamandojin da suka kwanta dama a wurin jana’izar.

Mutanen sun kuma riƙa daga hotunan mamatan a matsayin waɗanda suka yi mutuwar shahada, a yayin da suke la’antar Isra’ila da Amurka.

Daga cikin kwamandojin da Isra’ila ta kashen har da jagoran Rundunar Juyin Juya Halin Musulunci na Iran Janar Hossein Salami da Janar Amir Ali Hajizadeh da wani ƙwararren masanin kimiyyar makamashin nukiliya, Mohammad Mehdi Tehranchi.

Za a iya tuna cewa Amurka ta kai wa cibiyoyin nukiliyar Iran hare-hare a ƙarshen makon da ya gabata, kafin daga bisani a tsagaita wuta.

Amurka da Isra’ila sun yi iƙirarin cewa hare-haren sun yi gagarumar nasarar ruguza shirin kera makaman nukiliya na Iran.

Amma daga bisani Iran ta ƙaryata su, da cewa babu wata illa da hare-haren suka yi wa shirinta da makamashin nukiliya.

A ranar Talata Shugaban addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei ya karyata abin da ya kira kambama harin da shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya yi na cewa harin hare-haren sun mayar da shirin nukiliyar Iran baya da shekaru.

An kashe manyan sojojin da masa kimiyyar nukiliyar Iran ne a harin da Isra’ila ta fara kaiwa bisa hujjar neman daƙile shirin Iran na mallakar makamin nukiliya.