Gwamnatin Nijeriya ta ce babu wata barazanar tsaro a babban birnin ƙasar, Abuja, inda ta yi kira ga mazauna birnin su ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum cikin lumana.
Nijeriya ta musanta batun yiwuwar kai hari kan ’yan Amurka da suke zaune a kasar, sakamakon rikicin da ke faruwa a yankin Gabas ta Tsakiya.
- Mali ta ƙulla yarjejeniyar nukiliya da Rasha
- Trump ya soki Iran da Isra’ila kan saɓa wa yarjejeniyar tsagaita wuta
Gwamnatin ta bayyana haka ne a matsayin martani dangane da gargaɗin tsaro da Amurka ta aika zuwa ga ’yan ƙasarta da ke birnin Abuja.
A sanarwar da Ministan Watsa Labarai na Nijeriya, Mohammed Idris ya fitar, ya ce, “Gwamnatin Nijeriya ta samu labarin gargaɗin da Amurka ta aika wa ma’aikatan ofishin jakadancinta da ma ’yan ƙasarta da ke Abuja game da tsaro.
“Duk da Gwamnatin Nijeriya na girmama haƙƙin da ofisoshin jakadanci — ciki har da na Amurka — ke da shi na ba ’yan ƙasarta shawara ko gargaɗi game da matsalolin tsaro, yana da muhimmanci mu tabbatar da cewa babu wata barazanar tsaro da Nijeriya ke fuskanta, sannan mazauna birnin da masu ziyara babu wata barazana da suke fuskanta.”
Sanarwar ta ƙara da cewa babu dalilin wannan gargaɗi saboda akwai cikakken tsaro a Abuja, “domin jami’an tsaro suna aiki ba dare ba rana domin tabbatar da daƙile dukkan wata barazanar tsaro.”