✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Harin da Iran ta kai wa sansanin sojin Amurka keta haddin Qatar ne’

Mun tabbatar da cewa babu wanda ya rasa rai ko jikkata a harin.

Gwamnatin Qatar ta yi Allah-wadai da harin da Iran ta kai kan sansanin sojin saman Amurka da ke yankin al-Udeid na kasar.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar, Majed al-Ansari, ya wallafa a shafinsa na X cewa: “Mun ɗauki wannan a matsayin keta haddin Qatar da sararin samaniyarta da dokokin duniya da kuma yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya.”

Ya ce na’urorin kakkaɓo makamai na ƙasar sun “samu nasarar daƙile hare-haren na makamai masu linzami” kuma tuni aka janye dakarun Amurka daga sansanin tun kafin harin.

Ya ƙara da cewa “an ɗauki duka matakan da suka dace wajen tabbatar da tsaron lafiyar dakarun a sansanin, ciki har da sojojin Qatar, da dakarun ƙawance da sauransu.

“Mun tabbatar da cewa babu wanda ya rasa rai ko jikkata a harin.”

Kakakin ya ce Qatar na da damar mayar da martani “domin rama daidai da abin da aka yi mata.”

Rahotanni na cewa ƙasar Iran dai ta fara abin da ta kira martani mafi girma da nasara kan hare-haren Amurka.

Kamfanin Dillancin Labaran Iran na Tasnim, ya ce dakarun juyin juya halin ƙasar sun ƙaddamar da hare-haren makamai masu linzami kan sansanin sojin Amurka da ke Qatar da Iraƙi.

Sai dai majalisar tsaron Iran ta ce harin da ta kai sansanonin sojin Amurka da ke cikin Qatar ba shi da niyyar cutar da ƙasar.

Cikin wata sanarwa da majalisar ta fitar, ta ce Iran za ta ci gaba da martaba dangantar tarihin da ke tsakaninta da Qatar.

“Harin da muka kai ba ya ɗauke da wani hatsari ga mutanen Qatar, saboda ba ƙasar muka nufa ba”, in ji sanarwar.

Sanarwar ta ƙara da cewa “yawan makamai masu linzamin da aka yi amfani da su a harin sun yi daidai da adadin bama-boaman da Amurka ta yi amfani da su a cibiyoyin nukiliyar Iran uku.”

Qatar mai arzikin man fetur wadda ke da tazarar kilomita 190 da kudancin Iran, tana ɗauke da sansanin sojin Amurka na Al Udeid wanda shi ne mafi girma a yankin na Gulf.