Shugaban Ƙasar Rasha, Vladimir Putin, ya ce babu wata hujja ko dalilin kai wa Iran hari
Putin ya kuma ce harin babu gaira babu dalili da Amurka ta kai wa tashoshin nukiliya Iran yana kusanto da duniya zuwa cikin mugun yanayi, kana ya sha alwashin cewa zai yi ƙoƙarin taimaka wa Iran, sai dai bai fayyace irin taimakon ba.
Putin ya yi wannan furuci ne yayin wata tattaunawa da Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Agarachi a fadar Kremlin da ke birnin Moscow.
- Akwai ƙasashen da ke shirin bai wa Iran makaman nukiliya — Rasha
- Fararen hula sun yi garkuwa da sojoji 57 a Columbia
A jawabin da ya gabatar a farkon tattaunawar wanda aka yada a gidan talabijin na gwamnatin Rasha, shugaba Putin ya ce: “Babu wata hujja ko dalili da zai sa a kai wa Iran farmaki.”
Ya ƙara da cewa “na ji daɗin zuwan ka [Agarachi] Moscow a yau. Wannan zai ba mu damar tattauna waɗannan batutuwa masu wahala da kuma hanyar shawo kan lamarin.”
A nasa jawabin, Ministan Harkokin Wajen na Iran ya ce ƙasarsa na da “ƙawance ta ƙut da ƙut” da Rasha.
Ya ce hare-haren da Isra’ila da Amurka suka kai wa Iran “sun saɓa wa dokoki da ƙa’idojin ƙasa da ƙasa.”
A farkon shekarar nan Iran da Rasha sun sanya hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna.
Sai da ba ta haɗa da ƙawancen soji ba kuma ba ta buƙaci Rasha ta kai wa Iran ɗaukin kariya ba.