Manyan Hafsoshin Tsaro na ƙasar Iran sun sha alwashin mayar wa Amurka da martani mai tsanani wanda sai ta yi da-na-sanin harin da kai wa Iran.
Rundunar Tsaro ta Iran ta sanar da haka ne bayan wani zama da Babban Kwamandan Sojojin ƙasar, Amir Hatami, ya yi da wasu manyan kwamandojinsa.
Harami ya shaida wa taron tsare-tsaren cewa ya zama tilas Amurka ta girbi abin da ya shuka a Iran a wannan karon.
Ya bayyana cewa ko a baya, Iran ta saba koya wa Amurka darasi a duk lokacin da ta takali Iran.
- Koriya ta Arewa za ta taimaka da gyara tashoshin nukiliyan Iran —Masani
- NAJERIYA A YAU: Matakan daƙile kisan matafiya a hanyoyin Najeriya
Babban Hafsan Tsaron Iran, Abdolrahim Mousavi, a cikin wata sanarwa, ya ce, Iran ba za ta taɓa ja da baya ba, duk abin da Amurka za ta yi.