Shugaban Ƙasar Amurka Donald Trump ya ce an ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta gaba daya a yaƙin da ya ɓarke tsakanin Iran da Isra’ila.
Kafar yaɗa labarai ta the Guardian ta ƙasar Birtaniya ta ruwaito cewa Trump ya sanar da haka ne a shafinsa na sadar da zamunta, ’yan sa’o’i bayan hare-haren ramuwar gayya da Iran ta kai a sansanin sojin Amurka da ke ƙasar Qatar da Iran bayan hare-haren da Amirkan ta kai wa Iran.
Ya sanar cewa cikin awa shida na farko Iran za ta fara dakatar da kai hare-hare, daga bisani Isra’ila ta dakatar, wanda hakan zai kawo ƙarshen yaƙin ɗungurungum.
Sanarwar tasa na zuwa ne bayan tsohon Fira Ministan Rasha, babbar ƙawar Iran, Dimitry Medvedev na cewa ƙasashe masu ƙarfin makaman nukiliya na yi wa Iran tayin makaman nasu a yayin da yaƙin ke ƙara ƙamari.
- Babu dalilin kai wa Iran farmaki — Putin
- Akwai ƙasashen da ke shirin bai wa Iran makaman nukiliya — Rasha
Kazalika akwai yiwuwar babbar abokiyar gaban Amurka, wato Koriya ta Kudu na shirin taimaka wa Iran gyara tashoshin nukiliyan da hare-haren Amurka da Isra’ila suka shafa, da kuma gina sababbin masana’antun ƙera makamai masu linzami masu gudun walƙilya.
Hakan na zuwa ne kuma bayan Majalisar Dokokin Iran ta amince da ƙudirin rufe mashigar tekun Hormuz, matakin da Amurka ta buƙaci China ta sa baki Iran ɗin ta janye.
A gefe guda kuma Iran ta ci gaba da ruwan rokoki a kan Isara’ila, wadda ta fara kai wa cibiyoyin nukiliyar da na harkokin soji da fararen hula hari a ranar 13 ga watan nan na Yuni.