✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun amince da tsagaita wuta da Iran —Isra’ila

Isra'ila ta ce ta amince da shiga yarjejeniyar tsagaita wuta da Iran ce bayan abin da ya kira cimma burinta

Gwamnatin ƙasar Isra’ila ta ce ta amince da tsagaita wuta a yaƙin da aka kwana 12 ana gwabzawa tsakaninsu da Iran.

Isra’ila ta ce ta amince da shiga yarjejeniyar tsagaita wuta da Iran ce bayan abin da ya kira cimma burinta na ƙaddamar da yaƙin a Iran tun a farko.

Ta bayyana a cikin wata sanarwa cewa ta yi nasarar murƙushe duk wata barazanar da take fuskanta daga Iran na mallakar makamin nukiliya da makamai masu linzami.

Isra’ila ta ƙara da cewa ta kuma yi nasarar wargaza lissafin shugabancin sojin Iran da kuma lalata muhimman kadarorin gwamnatin ƙasar.

A karshe ta ce tanq godiya bisa abin da ya kira ƙoƙarin Shugaban Amurka Donald Trump na wargaza shirin nukiliyar Iran.