✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun yi wa ’yan bindiga luguden wuta a Neja

Sojojin sun kai harin ne a matsayin ramuwar gayya.

Sojojin Sama sun kai gagarumin farmaki sansanonin ’yan bindiga da ke Jihar Neja a ranakun Laraba da Alhamis.

Wannan farmaki na zuwa ne a matsayin ramuwar gayya bayan da ’yan bindiga suka kai hari kan wasu dakarun Najeriya a kwanan nan.

A cikin wata sanarwa da rundunar sojin sama ta fitar a shafinta na sada zumunta, ta bayyana cewa an kai harin ne a ƙarƙashin wani shiri da ake kira FANSAN YAMMA, wanda nufinsa shi ne kawar da barazanar da ’yan ta’adda ke haddasawa.

Sanarwar, wadda ta samu sa hannun Daraktan Yaɗa Labaran rundunar, Air Commodore Ehimen Ejodame, ta ce an samu bayanan sirri cewa ’yan bindigar suna satar shanu da kuma gudanar da wasu munanan ayyuka a yankunan Kakihun da Kumbashi.

Bayan haka ne sojojin sama tare da haɗin gwiwar sauran jami’an tsaro suka gano inda suke, kuma suka kai musu farmaki.

Sanarwar ta ce, “An kai hare-haren ne nan take, inda aka kashe ’yan fashin da dama, aka lalata kayayyakin da suke amfani da su, sannan aka hana su sake haɗuwa.”

A cikin makon nan ne rahotanni suka nuna cewa ’yan bindiga sun kai hari kan sansanin sojoji a Jihar Neja, inda suka kashe aƙalla jami’an soja 17.

Rundunar sojin ƙasa ta tabbatar da harin a wata sanarwa, amma ba ta faɗi adadin sojojin da suka mutu ba.

Jihar Neja na ɗaya daga cikin jihohin da ke fama da matsanancin matsalar tsaro, inda ’yan bindiga ke kai hare-hare.

Suna ƙone ƙauyuka da hallaka mutane da dama, lamarin da ke hana zaman lafiya da kuma lalata harkokin tattalin arziƙi a yankin.