Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai hari wasu ƙauyuka biyu da ke Ƙaramar Hukumar Kajuru a Jihar Kaduna.
A yayin harin, wata matar aure ta rasu, yayin da wani manomi ya samu rauni.
- ’Yan bindiga sun sace babban alƙali a Bayelsa
- Dole a ɗauki mataki kan waɗanda suka kashe ’yan ɗaurin aure a Filato — Uba Sani
Harin farko ya faru ne da misalin ƙarfe 2 na daren ranar Asabar, 21 ga watan Yuni, 2025, a ƙauyen Ungwan Sarkin Hausa da ke Rimau.
Ana zargin maharan sun gudu da shanun da suka sato daga Ƙaramar Hukumar Kauru.
A lokacin harin, sun kashe wata mata mai suna Misis Alheri Danzaria.
Sun kuma sace wasu mutum biyu, amma daga baya suka sake su.
Hari na biyu ya faru ne da safiyar ranar Lahadi da misalin ƙarfe 7 a ƙauyen Kallah.
A nan ne suka harbi wani manomi mai suna Mista Iliya Barde, yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa gona.
An garzaya da shi asibiti inda yake samun kulawar likitoci.
Shugaban gundumar Kufana, Mista Stephen Maikori, ya ce hare-haren da ake yawan kai wa sun haddasa tsoro da damuwa a tsakanin mazauna yankin.
Ya buƙaci gwamnati da ta ɗauki matakin gaggawa wajen ƙara tsaro a yankin.
Da aka tuntuɓi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Mansir Hassan, ya ce zai bincika lamarin sannan ya bayar da amsa, amma har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto bai yi ƙarin haske ba.