✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnonin Arewa sun yi Allah-wadai da kisan ’yan ɗaurin aure a Filato

Wasu ɓata-gari ne suka tare matafiyan tare da musu kisan-gilla.

Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya nuna baƙin cikinsa kan kisan wasu matafiya daga Jihar Kaduna da aka yi a Ƙaramar Hukumar Mangu ta Jihar Filato.

Matafiyan sun fito ne daga Zariya suna kan hanyarsu ta zuwa ɗaurin aure, yayin da wasu ɓata-gari suka farmake su.

Gwamnan ya ce wannan kisa abin takaici ne kuma rashin imani ne da ya saɓa wa doka.

Ya buƙaci a yi adalci cikin gaggawa.

Haka kuma ya miƙa ta’aziyyarsa ga Gwamnatin Jihar Kaduna, iyalan mamatan, da sauran waɗanda abin ya shafa.

A cewar sanarwar da Daraktan Yaɗa Labaran Gwamnatin Jihar Gombe, Isma’ila Uba Misilli, ya fitar, Gwamna Yahaya ya yaba wa gwamnati da ‘yan sanda a Jihar Filato bisa kamo wasu da ake zargi da hannu a kisan.

Gwamnan ya buƙaci a yi bincike na gaskiya, a gurfanar da waɗanda ke da hannu domin a hukunta su, sannan a hana irin hakan faruwa a gaba.

Haka kuma, ya roƙi al’ummar Filato da Kaduna da sauran maƙwabta da su zauna lafiya, su guji ɗaukar fansa.

Ya ce Gwamnonin Arewa za su ci gaba da haɗa kai domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a yankin.

“Ina tabbatar muku cewa kare rayuka da dukiyoyin al’umma shi ne babban burinmu. Za mu yi aiki tare har sai an kawo ƙarshen wannan matsala,” in ji Gwamnan.