✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

HOTUNA: Yadda aka yi jana’izar ’yan ɗaurin auren da aka kashe a Filato

Sai dai Gwamnatin Filato ta ce za a hukunta waɗanda suka aikata laifin.

An yi jana’izar ’yan ɗaurin auren da aka kashe a garin Mangu, da ke Ƙaramar Hukumar Mangu ta Jihar Filato.

Waɗanda aka kashe sun haɗa da maza, mata da yara.

Dukkaninsu mazauna unguwar Basawa-Anguwan Rimi ne da ke Ƙaramar Hukumar Zariya a Jihar Kaduna.

Sun tashi ne daga Zariya zuwa Ƙaramar Hukumar Qua’an Pan da ke Jihar Filato domin halartar ɗaurin aure, amma aka kai musu hari a hanya.

An yi jana’izarsu tare da birne su da yammacin ranar Asabar a maƙabartar Hayi, ƙarƙashin tsauraran matakan tsaro.

Malamai a Mangu sun ce iyalan mamatan sun amince a birne su a Filato domin kaucewa shiga tashin hankali a garinsu.

Kafin yi musu jana’iza, malamai sun roƙi Musulmai su ɗauki lamarin a matsayin ƙaddara daga Allah, su kuma guji ɗaukar doka a hannunsu.

Sheikh Suleiman Haruna, ɗaya daga cikin malamai a yankin da ya jagoranci jana’izar, ya buƙaci jama’a da su zauna lafiya tare da yin haƙuri da juna.

Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya yi Allah-wadai da harin, inda ya umarci jami’an tsaro da su kamo masu hannu a lamarin.

Ga hotunan yadda jana’izar ta wakana: