✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dole a ɗauki mataki kan waɗanda suka kashe ’yan ɗaurin aure a Filato — Uba Sani

Ya sha alwashin cewa gwamnatin jihar ba za ta gajiya ba har sai ta ga an gurfanar da maharan.

Gwamnan Kaduna, Uba Sani ya buƙaci a ɗauki mataki kan kisan wasu ’yan jiharsa mutum 12 a Ƙaramar Hukumar Mangu ta Jihar Filato a hanyarsu ta zuwa ɗaurin auren ɗan uwansu.

Aminiya ta ruwaito cewa an kashe mutum 12 yayin da wasu 11 suka jikkata daga cikin mutum 31 da suka taso daga garin Basawa da ke Ƙaramar Hukumar Zaria a Jihar Kaduna cikin motar bas mallakin Jami’ar ABU Zaria, kafin su faɗa hannun maharan.

Gwamna Uba Sani wanda ya yi Allah-wadai ya nuna kaɗuwarsa matuƙa kan lamarin a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya umarci jami’an tsaro da su gaggauta kama waɗanda suka aikata laifin da kuma hukunta su.

Ya sha alwashin cewa gwamnatin jihar ba za ta gajiya ba har sai ta ga an gurfanar da maharan.

“Lokaci ya yi da za mu kawo ƙarshen irin waɗannan abubuwa na kashe mutanen da ba su yi laifin komai ba, musamman yayin tafiya tsakanin jihohi.

“Babu wata hujja ta far wa kowane ɗan Nijeriya a kowane ɓangare na ƙasar. Ya kamata mu dakatar da wannan ɗanyen aiki,” in ji gwamnan.

Ya kuma jajanta wa iyalan waɗanda lamarin ya shafa, inda ya yi kira ga al’ummar jihar da su kwantar da hankali domin ana ƙoƙarin ganin an hukunta masu laifin.