✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnan Kaduna ya bai wa sabon Sarkin Moro’a sandar mulki

Sabon Sarkin ya yi alƙawarin yin mulki cikin gaskiya da amana.

Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya bai wa sabon Sarkin Moro’a, Mai Martaba Isiaku Tagwai Sambo sandar mulki, a wani biki da aka gudanar a garin Manchok da ke Ƙaramar Hukumar Kaura.

Gwamna Sani, ya bayyana cewa sarakunan gargajiya na taka muhimmiyar rawa wajen zaman lafiya, haɗin kai da kuma ci gaban al’umma.

Ya ce gwamnatinsa na bai wa sarakunan gargajiya cikakken goyon baya saboda irin rawar da suke takawa a harkar mulki da ci gaban jama’a.

“Mun jajirce wajen haɗa kan al’umma a faɗin Jihar Kaduna, ba tare da nuna bambanci ba.

“Yanzu Jihar Kaduna ta fi samun tsaro da kwanciyar hankali fiye da da. Wannan nasara ta samuwa ne sakamakon gudunmawar sarakunan gargajiya,” in ji Gwamnan.

Ya kuma buƙaci al’ummar jihar da su zauna lafiya da juna tare da yin aiki tare domin ciyar da jihar gaba.

Haka kuma, ya roƙi sarakunan da su ci gaba da jagorantar al’ummominsu cikin adalci da riƙon amana.

Bikin naɗin sarautar ya samu halartar baƙi daga sassa daban-daban, bayan rasuwar tsohon Sarkin Moro’a, Malam Tagwai Sambo, wanda ya rasu ranar 14 ga watan Yuni 2024.

Tsohon Sarkin ya rasu yana da shekaru 88, bayan mulkin shekaru 58.

Sabon Sarkin, Mai Martaba Isiaku Tagwai Sambo, ya gode wa gwamnati da al’ummar Moro’a bisa amincewar da suka yi masa.

Ya yi alƙawarin mulki cikin gaskiya da riƙon amana tare da bin doka da oda.

“Zamu haɗa kai da majalisar masarauta da kuma ɗaukacin al’umma domin tafiyar da wannan mulki yadda ya kamata,” in ji shi.