Aisha ta koma gidan mijinta, marigayi Muhammadu Buhari da ke Jihar Kaduna, bayan shafe kwanaki a Daura tana karɓar gaisuwa.
Mataimakiyar Gwamnan Jihar Kaduna, Dakta Hadiza Sabuwa Balarabe, ce ta jagoranci tawagar gwamnatin jihar wajen tarbar Aisha a Filin Jirgin Sama na Kaduna a ranar Lahadi.
- Tsohon shugaban jami’ar Kashere ya rasu a Abuja
- Gwamnatin APC ta jefa ’yan Najeriya cikin ƙangin talauci — Shugabar LP
Daga cikin waɗanda suka tarbe ta akwai Shugabar Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Munira Suleiman Tanimu, da wasu manyan jami’an gwamnati.
Tarbar da aka yi mata ta nuna yadda jihar ke ci gaba da girmama tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da iyalinsa bisa gudunmawar da suka bayar wajen ci gaban ƙasar nan.
Bayan tarbar ta, Dakta Hadiza ta raka Aisha Buhari da iyalanta zuwa gidan marigayin.
Wannan ya nunacewar iyalan marigayin za su ci gaba da rayuwa a jihar, tare da ƙarfafa zumunci tsakanin gwamnatin jihar.
Dubban mutane na ci gaba da miƙa ta’aziyyarsu kan rasuwar tsohon shugaban wanda ya mulki Najeriya sau biyu.
Ga hotunan a ƙasa: