Shugaban Ƙasar Gambiya, Adama Barrow, tare da matarsa Fatoumata Barrow, sun ziyarci Jihar Katsina, inda suka yi ta’aziyyar rasuwar tsohon shugaban ƙasa, marigayi Muhammadu Buhari.
Sun kai ziyarar ne a ranar Juma’a domin jajanta wa iyalan marigayin game da rashin da suka yi.
- Za a ɗauke wuta na tsawon kwanaki 25 a Legas — TCN
- Wani mutum ya buɗe Ofishin Jakadancin Indiya na bogi a ƙasar
Sun sauka a filin jirgin sama na Umaru Musa Yar’adua da ke Katsina, inda Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Barista Abdullahi Faskari, ya tarbe su a madadin Gwamna Dikko Umar Radda.
Bayan sojoji sun yi wa Shugaba Barrow faretin ban girma, sun wuce Daura kai-tsaye, inda suka yi wa iyalan marigayin da kuma Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Faruk Umar Faruk ta’aziyya.
Ga hotunan a ƙasa: