✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnan Katsina ya tsallake rijiya da baya a hatsarin mota a hanyar Daura

Abokin tafiyar Gwamnan Kastina Dikko Raɗɗa da ɗaukacin fasinjojin motar da ta yi karo da tasu sun samu karaya shi kuma gwamnan ya samu buguwa…

 Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Raɗɗa ya tsallake rijiya da baya bayan motarsa ta yi taho-mu-gama da wata mota a daren Lahadi a hanyarsa ta komawa Kastina bayan kammala ziyarar jana’izar tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a Daura.

Babban Sakataren Yaɗa Labaran gwamnan, Ibrahim Muhammad Kaula ya bayyana cewa wani ɗan Majalisar Tarayya da ke tare da Gwamna Raɗɗa a lokacin ya samu karaya a hatsarin.

Ya ƙara da cewa Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Jihar Katsina, Abdulƙadir Mamman Nasir, ma ya samu raunuka a hatsarin amma gwamnan bai samu wasu raunuka masu tsanani ba.

Rahotanni sun bayyana cewa Gwamna Raɗɗa ya samu buguwa a ƙirji, amma Sakataren Yaɗa Labaran ya ce, tuni gwamnan ya samu kulawar likita kuma har ya ci gaba da harkokinsa.

Shaidun gani da ido sun ce a yammacin ranar Lahadi ne wata motar haya ƙirar Gulf ta yi taho-mu-gama da motar da gwamnan, kuma ɗauƙacin fasinjojin cikin Gulf ɗin sun samu karaya.

Ana zargin motar da ta yi karo da ta gwamnan ta ƙwace wa direbenta ne saboda lodinta ya wuce misali, da kuma yadda aka sanya mutane a kowane gefe na direban.

Rahotannin sun bayyana cewa, motar gwamna ba ta taho a bisa tsarin tafiyar da aka saba ta gwamnati ba, wadda ke cike da matakan tsaro da kuma masu kula da yanayin tafiya.