Gomman mutane da iyalan tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari sun gudanar masa da addu’ar sadakar uku, a gidansa da ke Daura, Jihar Katsina.
Taron addu’ar ya samu halartar manyan shugabanni, malaman addini da baƙi daga sassa daban-daban na ƙasar nan.
- Ambaliya ta karya gadar Oji, matafiya sun maƙale a Gombe
- Hauhawar farashi ya sauka zuwa kashi 22.22 a watan Yuni — NBS
Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a wajen addu’ar.
Haka kuma tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, da Peter Obi na daga cikin manyan baƙin da suka halarta.
Sarkin Malamai na Daura, Malam Naziru Daura ne ya jagoranci addu’ar, inda ya yi wa marigayin addu’ar neman gafara a wajen Allah.
Malaman addini da suka halarta sun yi addu’o’i na musamman, inda suka roƙi Allah Ya gafarta masa, ya kuma jiƙansa da rahama, ya kuma bai wa iyalansa haƙurin rashina.
Kashim Shettima ya ce: “Duk rai ɗaya ne, kuma mutuwa makoma ce da babu makawa. Dole ne kowa ya mutu.
“Allah Ya gafarta wa Shugaba Muhammadu Buhari, ya saka masa da alheri, ya kuma kare iyalansa. Wannan babban rashi ne, ba ga iyalansa kawai ba, har da mutanen Daura, Katsina da ma Najeriya baki ɗaya.”
A nasa jawabin, Gwamna Dikko Radda, ya bayyana cewa marigayin jagora ne kuma uba ne ga al’ummar Jihar Katsina.
Ya ce: “Mun yi rashin mutum mai taimako, kuma abin da ya rage mana yanzu shi ne mu ci gaba da yi masa addu’a, mu kuma nemi Allah Ya gafarta masa duk wani kuskuren da ya yi.
“Haka kuma shugabanni su dinga tunani a kan mutuwa, domin hakan zai sa su ji tsoron Allah a mulkinsu.”
An kammala addu’ar cikin kwanciyar hankali da nuna girmamawa ga marigayin, inda jama’a suka ci gaba da roƙon Allah Ya jiƙan Muhammadu Buhari.