A yau Talata, 15 ga watan Yulin 2025, aka gudanar da jana’izar tsohon Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari a gidansa da ke garin Daura na Jihar Katsina.
An binne gawar marigayi Muhammadu Buhari ne da misalin karfe shida na yamma a agogon Nijeriya bayan kai ta Daura daga filin jirgin saman birnin Katsina.
Aminiya ta ruwaito cewa Buhari ya rasu ne a birnin Landan ranar Lahadi yana da shekaru 82 a duniya.
Dubban mutane ne suka halarci jana’izar ciki har da Shugaba Bola Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima da sauran manyan mutane daga ciki da wajen Nijeriya.
Haƙiƙa wannan mutuwa ce da ta kaɗa duk wanda ya ji ta, walau masoyi ko maƙiyin Buhari, duk da cewa an ji labarin jinyarsa a asibiti a Birtaniya mako kusan biyu da suka wuce.
Iyalan marigayin ne suka sanar da rasuwarsa a shafukansa na sada zumunta a ranar Lahadin, kamar yadda mai taimaka masa a yaɗa labarai, Garba Shehu ya sanya hannu kan sanarwar.
Tsohon shugaban ya mulki Nijeriya tsakanin 1983 zuwa 1985 a matsayinsa na soja. Sannan kuma an zabe shi a matsayin shugaban ƙasa na mulkin farar hula daga 2015 zuwa 2023. Kafin zabensa, ya rike manyan makamai a ƙasar.
Haihuwa, tasowa da karatun Buhari
An haife shi a ranar 17 ga watan Disamban 1942 a karamar hukumar Daura da ke Jihar Katsina.
Mahifinsa wanda Bafulatani ne ya rasu tun lokacin da Buhari ke da shekara huɗu a duniya, inda ya girma a hannun mahaifiyarsa ’yar ƙabilar Kanuri.
A wata tattaunawa cikin shekara ta 2012, Buhari ya faɗi cewa shi ne na 23 a cikin ’ya’yan mahaifinsa, kuma na 13 a wurin mahaifiyarsa.
Ya bayyana cewa abin da kawai zai iya tunawa game da rayuwa tare da mahaifinsa shi ne wani lokaci da doki ya kayar da su, shi da mahaifinsa da wani ɗan uwansa.
Muhammadu Buhari ya halarci makarantar allo sannan ya yi kiwon shanu, kafin ya shiga makarantar firamare.
Ya fara karatunsa na matakin farko tsakanin Daura da Maiduguri cikin shekarun 1948 zuwa 1952, ya wuce Katsina Middle School a 1953, sannan ya halarci makarantar Sakandare provincial da ke Katsina a tsakanin 1956 zuwa 1961, a nan ne ya samu takardar shaidar sakamakon jarabawar kammala karatu ta yammacin Afirka da a yanzu ake kira WAEC.
Daga nan ne ya shiga kwalejin horas da kananan hafsoshin soji a 1962.
Tsakanin 1962 zuwa 1963, marigayin ya je karin horon aikin soji a kwalejin Mons Officer Cadet da ke Aldershot a Ingila.
Janar Olusegun Obasanjo ya zaɓe shi a matsayin kwamishinan tarayya na man fetur, inda a shekarar 1977, aka naɗa shi sakataren Majalisar ƙolin sojin ƙasar, kafin daga bisani ya riƙe muƙamin babban kwamandan sojoji na Kaduna.
Ya zama shugaban kasa ta hanyar juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Disamba 1983, amma cire shi daga mukaminsa a wani juyin mulki da ya wakana a watan Agustan 1985.
Marigayin ya fara shiga siyasa ne a 2003, lokacin da yayi takarar shugabancin ƙasar da Olusegun Obasanjo, amma ya kayar da shi karkashin jam’iyyar PDP.
Ya kara neman kujerar shugabancin ƙasar a shekarar 2007, amma Umaru Yar’Adua ƙarƙashin jam’iyyar PDP ya kayar da shi, inda ya sake tsayawa wata takarar a shekarar 2011 tare da tsohon shugaba Goodluck Jonathan, amma bai samu nasara ba.
Sai a 2015 ne ya samu nasara a babban zaɓen ƙasar karkashin jam’iyyar APC, yayin da ƙuri’un da aka kaɗa masa suka zarce na Jonathan da yawansu ya tasamma miliyan 2.5.
A ranar 29 ga watan Mayun 2015 aka rantsa da shi a matsayin shugaban ƙasa, kuma bayan ƙare wa’adi na farko, ya sake lashe babban zaɓen ƙasar a shekarar 2019.
Yaƙin basasa
A matsayinsa na soja, Buhari na cikin dakarun da suka fafata da na ‘yan-a-waren Biafra.
Bayan kammala yaƙin kuma ya ci gaba da zama sojansa har ma ya yi ta zuwa samun ƙarin horo a ciki da wajen Nijeriya da ma samun girma.
Gwagwarmayar zama shugaban Nijeriya sau biyu
Muhammadu Buhari ya fara yi wa ƙasarsa ta Nijeriya hidima ne a matsayin soja, inda ya samu damar zama Shugaban Ƙasa har sau biyu.
Karon faro ya yi shugabancin ne a matsayin Shugaban Ƙasa na mulkin soja, daga 31 ga Disamban 1983 zuwa 27 ga Agustan 1985.
A karo na biyu kuwa, ya karbi ragamar mulkin Nijeriya a ƙarƙashin tsarin dimokuraɗiyya, shekara 30 bayan mulkin soja da ya yi.
An zaɓi Buhari ƙarƙashin jam’iyyar APC bayan da ya kayar da shugaba mai ci Goodluck Ebele Jonathan a 2015.
Wannan zaɓe yana daga cikin mafiya tarihi da aka yi a Nijeriya, musamman ganin irin guguwar zaɓen Buharin da aka yi da kuma tashin hankalin da aka shiga na fargabar abin da zai faru idan “aka murɗe” zaɓen ya faɗi kamar yadda da yawa suka yi ta zargin za a yi.
Sai dai a wa’adin farko na mulkin nasa na farar-hula, ya yi ta fama da jinya inda ya dinga tafiya Birtaniya, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce mai yawa a ciki da wajen ƙasar.
Ya sake tsayawa takara a 2019 bayan kammala wa’adin farko, kuma ya yi nasarar hayewa inda ya ƙare wa’adi na biyu a watan Mayun 2023.
Tun sannan ne kuma ya koma mahaifarsa Daura da zama, har sai a farkon 2025 ne sannan ya sake komawa Kaduna, inda dama a can yake zama kafin ya zama Shugaban Ƙasa.
Buhari da Obasanjo ne kawai shugabannin Nijeriya da suka taɓa yin mulki sau biyu, kuma dukkansu a matsayin soja da farar-hula.
Juyin Mulki
Wani lamari na tarihi da ba za a manta Buhari da shi ba shi ne lamarin juyin mulki da ya shafe shi har sau biyu.
Ɗaya shi ne ya yi, ɗayan kuma shi aka yi wa. A watan Disamban 1983, Manjo Janar Muhammadu Buhari ya kasance ɗaya daga cikin jagororin juyin mulkin da ya kifar da gwamnatin Jamhuriyya ta biyu ta Shugaban Ƙasa Shehu Shagari.
Wannan nasara ce ta kai Buhari ga ɗarewa mulki. Sai dai shi ma a watan Agustan 1985, sai aka tumɓuke shi daga mulkin ƙasar bayan wani juyin mulki da Manjo Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya yi masa.
Bayan nan kuma Buhari ya shafe shekara uku a tsare lokacin da shi kuma Babangidan yake mulkin ƙasar.
Yaƙi da Rashin Ɗa’a
Wataƙila babban abin da tarihi ba zai manta game da mulkin Janar Buhari ba a zamanin mulkinsa na farko shi ne yadda ya ɓullo da shirin ‘War Against Indiscipline’, wato ‘Yaƙi da Rashin Ɗa’a’.
An ƙaddamar da shirin ne a watan Maris ɗin 1984 har zuwa watan Satumban 1985.
Maƙasudin shirin shi ne gyara tarbiyyar ‘yan ƙasa ta zamantakewa da sauran mu’amaloli, kamar hana zuwa wajen aiki latti da cin amana da sauran munanan ayyuka.
A tsawon lokacin da Buhari ya mulki Nijeriya a matsayin soja, abubuwa da dama sun sauya.
Abin da aka fi tunawa kan mulkin nasa na farko su ne tsarinsa na yaƙi da rashin ɗa’a, sai kuma yaƙi da rashawa.
Kimanin ’yan siyasa 500 ne gwamnati ta ɗaure a wani mataki na yaƙi da rashawa da ɓarnata dunkiyar al’umma.
Wasu sun kalli waɗannan tsare-tsare na gwamnatin Buhari a matsayin kama-karya, wasu kuma na kallon hakan a matsayin abin a yaba wajen yaƙi da rashawa, abin da ya yi wa ƙasar katutu kuma yake hana ta ci gaba.
Waɗannan matakai na daga cikin abubuwan da suka sa Buhari ya samu laƙabin mai gaskiya.
A wani ɓangare na shirin yaƙi da rashin ɗa’a, an tursasa wa mutane bin layi a wurin hawa mota, an kuma tursasa wa waɗanda ake zargi da ɓoye kaya fitowa da su su sayar.
An kuma riƙa hukunta ma’aikatan gwamnati da ke zuwa ofis a latti, cikin irin wannan hukunci har da tsallen kwaɗo.
Sauye-sauye ne da ba a saba gani ba, sai dai wasu sun ce lamarin ya zama tamkar danniya, musamman ƙoƙarin da gwamnatin ta yi na samar da dokar taƙaita ’yancin ’yan jarida.
Wani abu da ake tunawa da shi a cikin matakan da gwamnatin Buhari ta wancan lokaci ta ɗauka shi ne sauya takardar naira, inda aka ƙayyade lokacin da mutane za su iya sauya tsofaffi da sabbi.
Haka nan an kulle shahararren mawaƙin nan Fela Kuti bisa zargin safarar kuɗi.
Ɗauri bayan juyin Mulki
Bayan shafe wata 20 a kan Mulki, abubuwa sun yi ƙamari, kuma a wannan lokaci ne aka tuntsurar da gwamnatin Buhari, inda Janar Ibrahim Babangida ya karɓi mulki.
Bayan hamɓarar da shi ne kuma aka kulle shi har tsawon wata 40 a garin Benin City.
An saki Muhammadu Buhari a watan Disamban 1988, bayan rasuwar mahaifiyarsa.
Asusun Rarar Man Fetur (PTF)
Tun bayan sakin sa, Muhammadu Buhari ya koma yin rayuwa mai sauƙi.
Kusan an daina jin ɗuriyarsa har sai lokacin da shugaban mulkin soji na Najeriya Sani Abacha ya naɗa shi shugaban Asusun Rarar Man Fetur na Najeriya (PTF).
Asusun na samu kuɗinsa ne daga rara da aka samu bayan ƙara farashin man fetur, inda ake amfani da kuɗaɗen wajen ayyukan raya ƙasa.
An bayyana PTF a matsayin shiri wanda ya yi nasara, sanadiyyar irin tallafin da shirin ya bayar a ɓangarori daban-daban na ci gaban ƙasa.
Farin Jini
Idan aka ce ba a taɓa samun wani Shugaban Ƙasa ko kuma ɗan takarar Shugaban Ƙasa da ya yi irin farin jinin Buhari ba na tabbata ba a za musa ba.
Shugaba Buhari ya kasance mai tsananin farin jini a wajen al’ummar Nijeriya musamman ma talakawa.
Farin jinin nasa ma ya fi shahara ne a lokacin da ya tsaya takarar Shugaban Ƙasa na farar-hula musamman daga 2011 zuwa na 2015.
Da ya faɗi zaɓe a 2011 har wata tarzoma sai da ta tashi a yankin arewacin ƙasar, inda mutane suka ƙi yarda da sakamakon zaɓen.
A 2015 kuwa da ya ci zaɓe, tsabar bikin murna da mutane suka dinga yi sai da aka samu waɗanda suka rasa rayukansu sakamakon wasa da ababen hawa da suka dinga yi ba ji ba gani.
Shi ne kuma ɗan takara ɗaya tilo da har kuɗin yaƙin neman zaɓe sai da mutane suka dinga haɗa masa.
Takarar Shugaban Kasa sau huɗu
Muhammadu Buhari yana daga cikin mutane ƙalilan da suka jajirce wajen neman mulkin Nijeriya a ƙarƙashin mulkin farar hula suna faɗuwa. Amma Buhari bai sare ba sai da ya samu.
Ya fara tsayawa takara ƙarƙashin Jam’iyyar ANPP a shekarar 2003 inda ya kara da shugaba mai ci a lokacin Olusegun Obasanjo, amma
ya sha kaye.
Ya tsaya a 2007 a ANPP tare da Umaru Musa ‘Yar’adua na PDP, Buhari ya sake shan kaye.
Buhari ya jajircewa ya ƙi sallamawa, ya sake tsayawa a 2011 a Jam’iyyar CPC, a nan ma ya sha kaye a hannun Goodluck Ebele Jonathan.
A karo na huɗu na tsayarwa takara, sai Allah Ya bai wa Buhari nasara inda ya lashe zaɓen a 2015 ƙarƙashin Jamiyyar APC.
A dukkan waɗannan lokuta da ya fadi zaɓe, sau uku yana danganawa da kotu amma ba a taɓa rushe zaɓukan an ba shi ba.
Shaidar rashin cin hanci
Wata shaida da aka yi wa Buhari ita ce ta gaskiya da rashin cin hanci da rashawa wadda ko a cikin sakonnin alhini da manyan ’yan siyasar Nijeriya suka rika fitarwa sun tabbatar da hakan.
Har wani take ake masa da har a waƙa sai da aka sa, wato “Yau Nijeriya riƙo sai mai gaskiya, sannu Buhari kai muke so Nijeriya.”
Sannan aƙidarsa ta yaƙi da cin hanci da ya kaddamar tun a zamaninsa na mulkin soja ta sake fito da wannan hali nasa.
A lokacin mulkinsa na soja, Buhari ya yi ƙaurin suna wajen aniyarsa ta yaƙi da cin hanci da rashawa, inda aka riƙa kama mutanen da duk ake zargi da yin cin hanci a gwamnatin hamɓararren Shugaba Shehu Shagari, tun daga kan ministocinsa da jami’an gwamnati da ‘yan kasuwa har ma da sarakuna.
An yanke wa wasu hukuncin daurin rai da rai, wasu kuma daurin zaman gidan yari na shekaru da dama, da makamantansu.
An kuma sake yi masa irin wannan shaidar a lokacin da ya riƙe shugabancin hukumar Petroleum Trust Fund ta Nijeriya lokacin mulkin marigayi Janar Sani Abacha.
Kazalika, badaƙalar da aka bankaɗo a farkon hawa mulkinsa na farar-hula, har ta dala biliyan biyu ta kuɗaɗen makamai a gwamnatin Jonathan, sakamakon wani kwamiti da Buharin ya naɗa don yin bincike, ta sake kankaro masa “martaba da mutunci a idon ‘yan Nijeriya”.
Jinya
Bayan cimma burinsa na komawa kan mulki, wani babban ƙalubale da Buhari ya ci karo da shi shi ne rashin lafiya da ya addabe shi.
Rashin lafiyar ya sanya Buhari ya kwashe lokaci mai yawa a cikin mulkin nasa wajen neman magani, musamman a wa’adin mulkinsa na farko.
Akwai lokacin da ya kwashe kwana 50 a birnin Landan yana jinya.
Wasu na ganin cewa rashin lafiyar marigayin ta taka rawa sosai wajen gaza cimma wasu daga cikin alƙawurran da ya ɗauka.
Sai dai a tsawon mulkinsa, rashin lafiyar Buhari ta zama sirrin da babu wanda ya sani, sai dai ko ƙila makusantan shi.
‘Duk wanda na ɓatawa ina neman gafara’
Da wadannan da ma wasu da dama, haƙiƙa tarihin Nijeriya kanta ba zai taɓa kammala ba sai da sunan Muhammadu Buhari a ciki.
Kuma mutane da dama ba za su manta da wani saƙonsa na Ƙaramar Sallar 2023 ba, wacce ita ce sallah ta ƙarshe da ya yi a matsayin shugaban Nijeriya.
Wata sanarwa daga Fadar Shugaban Ƙasar a lokacin, ta ambato Shugaba Buhari yana cewa: “Allah ya ba ni wata dama ta musamman ta yi wa kasar nan hidima.
“Dukkanmu ‘yan’adam ne, idan na ɓata wa wani yayin da nake yi wa ƙasa hidima, ina neman a gafarce ni.”
Muhammadu Buhari ya rasu ya bar mace ɗaya — Aisha Halilu wadda aka fi sani da Aisha Buhari wadda ita ce za ta yi masa takaba — da ’ya’ya 10 da jikoki da dama. Akwai kuma tsohuwar matarsa, Safinatu Yusuf wadda suka rabu a baya.