✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kai gawar Buhari Daura

Za a gudanar da sallar jana’iza sannan a binne shi a gidansa.

Gawar marigayi tsohon Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ta isa mahaifarsa Daura inda za a yi jana’iza da kuma binnewa.

Gawar wadda aka ɗauko daga filin jirgin saman Katsina bayan isowarta daga Landan ta samu rakiyar Shugaba Bola Tinubu, da mataimakinsa Kashim Shettima, da uwargidan marigayin, Aisha Buhari da kuma wasu daga cikin iyalansa.

Za a gudanar da sallar jana’iza sannan a binne shi a gidansa.

Mahaifar marigayin na cike da mutane waɗanda suka shafe sa’o’i suna dakon jiran isowar gawar domin yi mata Sallah.

Iyalai da ’yan uwa masu bankwana da mamacin sun taru a jikin motar ɗaukar gawar, inda suke kuka tare da yi masa addu’a.

Bayan kammala addu’a ne za a ɗauki mamacin zuwa inda za a yi masa sallah kafin a sake mayar da gawar gida inda za a binne ta.

Ga wasu hotunan isowar gawar zuwa gidan marigayi Buhari