Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero da Sarkin Daura da ministoci da gwamnoni sun yi wa gidan tsohon Shugaban Kasa Muhamamdu Buhari tsinke domin ta’aziyya da jana’izar tsohon shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari a gidansa da ke Daura, Jihar Katsina.
Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed da minita Suwai da tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi da tsohon Ministan Sadarwa Isa Ali Pantami, da manyana jami’an gwamnati na daga cikin wadanda Aminiya ta lura sun zo ta’aziyyar