Jirgin Fadar Shugaban Ƙasa ya ɗauko gawar tsohon Shugaban Ƙasa Marigayi Janar Muhammadu Buhari daga Landan.
A safiyar Talatar nan Mataimakin Shugaban da sauran ’yan rakiya suka taso a jirgin ɗauke da gawar Buhari wanda ya rasu a asibitin da yake jinya a can a ranar Lahadi.
Kakakin Buhari, Malam Garba Shehu, ya bayyana cewa gawar za ta iso Najeriya kafin Azahar kuma a gida za a binne Buhari.
Garba Shehu ya ce an fara aikin gina kabarin, amma sai nan gaba za a sanar da inda za a yi sallar jana’izar Buhari.
Wakilinmu ya yi kokarin isa wurin, amma jami’an tsaro sun hana.
Bayan isowar gawar Najeriya za a kai ta mahaifar Buhari da ke Daura a Jihar Katsina, inda za a gudanar da Sallar Jana’iza tare da kai shi makwancinsa.
Tuni an riga an tsara rumfuna da ke sa rana a nan Shugaba Tinubu zai karɓi gaisuwar ta’aziyya.
Aminiya ta ruwaito cewar Tinubu da kansa zai karɓi gawar kafin a yi mata ta’aziyya.
Buhari ya rasu yana da shekaru 82, shekara biyu bayan ya miƙa mulki ga shugaban kasa mai ci, Bola Ahmed Tinubu.