Tun bayan sanar da rasuwar tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, jama’ar garin Daura suka shiga cikin wani yanayi na rashin walwala da tsayawar sauran harkokin yau da kullum saɓanin yadda da aka saba.
Garin wanda aka sani da cinkoson jama’a a bisa manyan tituna da sauran wuraren harkokin kasuwanci a yanzu ya nuna tabbas ana cikin juyayin rashi.
- Gwamnatin Katsina ta ba da hutun jimamin rasuwar Buhari
- Majalisa ta tafi hutun sati 2 domin juyayin rasuwar Buhari
Ita ma fadar Mai Martaba Sarkin Daura, Dokta Farouk Umar Farouk wadda ake hada-hadar fadanci a cikinta, a wannan rana ta Litinin sai da sarkin ya fito zaman fada amma babu yawan mutanen da aka saba gani.


Shi kansa gidan marigayin da ke bisa hanyar zuwa Mai Aduwa babu mutane domin jami’an tsaro ba su barin a kusanci wurin da yake.
Ana dai sa ran kawo gawar marigayi Buhari a gobe Talata daga ƙasar Birtaniya domin yi mata jana’iza, kamar yadda mai magana da yawun Gwamnatin Katsina, Ibrahim Kaula ya sanar.