Rahotanni na cewa da misalin ƙarfe 2:00 na ranar gobe Talata za a yi jana’izar tsohon Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari.
Hakan na ƙunshe cikin wani jawabi da Gwamnan Katsina, Dikko Umar Radda ya yi wa manema labarai a wannan Litinin ɗin.
- HOTUNA: Yanayin garin Daura gabanin isowar gawar Buhari
- Gwamnatin Katsina ta ba da hutun jimamin rasuwar Buhari
Gwamna Radda ya ce, an cimma yarjejeniyar da iyalan marigayin kuma ana sa ran isowar gawarsa a gobe, “kuma abin da shawara ta kaya shi ne za a binne shi cikin gidansa da ke Daura,” in ji shi.
A cewarsa, ana sa ran gawar tsohon shugaban ƙasar za ta iso filin tashi da saukar jiragen sama na Katsina da misalin ƙarfe 12:00 na rana gabanin garzayawa da ita garin Daura inda za a yi jana’izar.
A jiya Lahadi ne dai aka sanar da rasuwar tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari.
Sanarwar da mai magana da yawunsa, Mallam Garba Shehu ya fitar, ta ce tsohon shugaban ya rasu ne a wani asibiti da ke Birnin Landan na ƙasar Birtaniya.