✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

HOTUNA: Tinubu ya kafa kwamitin jana’izar Buhari

An dora wa kwamitin nauyin shiryawa da tsara yadda jana’izar ƙasa ta musamman da za a yi wa mamacin.

Gwamnatin Tarayya bisa amincewar Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ƙaddamar da kwamitin da zai jiɓinci jana’izar ƙasa da za a yi wa tsohon Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari wanda ya riga mu gidan gaskiya a jiya Lahadi.

Kwamitin wanda Sakataren Gwamnatin Tarayya Sanata George Akume CON zai jagoranta an dora masa nauyin shiryawa da tsara yadda jana’izar ƙasa ta musamman da za a yi wa mamacin.

Sauran mambobin kwamitin sun hadar da Ministan Kudi da Tsare-Tsare da Ministan Tattalin Arziki da Ministan Kasafin Kudi da kuma Ministan Tsaro.

Akwai kuma Ministan Labarai da Fadakar da Al’umma da Ministan Ayyuka da Ministan Harkokin Cikin Gida da Ministan Abuja da Ministan Gidaje da kuma Ministan Lafiya da Ministar Al’adu.

Kazalika, kwamitin ya hadar da Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara Kan Tsaron Kasa da Sufeto Janar na ’Yan sanda da Babban Hafsan Dakarun Sojin Nijeriya da Darakta Janar na Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS). Sai kuma Babban mashawarci na musamman ga shugaban kasa kan harkokin siyasa da takwaransa na harkokin tsare-tsare.

Wata sanarwa da daraktan yada labarai da harkokin jamaa na Ofishin Sakataren Gwamnatin, Segun Imohiosen ya fitar ta ce shugaba Tinubu ya ba da umarnin bude rajistar manyan bakin da za su halarci janaizar marigayi Buhari.