A ranar Lahadi 13 ga watan Yuli, 2024, Allah Ya yi wa tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari rasuwa.
Buhari ya rasu yana da shekara 83 a yayin da yake jinya a Asibitin Birnin Landan da ke ƙasar Birtaniya.
Rasuwarsa ta auku ne shekara biyu bayan saukarsa daga mulki a matsayin zaɓaɓɓen shugaban Najeriya.
Tarihin rayuwarsa
An haifi Muhammadu Buhari ne a ranar 17 ga watan Disambar 1942, a garin Daura da ke Jihar Katsina.
- NAJERIYA A YAU: Abin Koyi Daga Rayuwar Marigayi Muhammadu Buhari — Makusantansa
- Tsoffin zaɓaɓɓun shugabannin Najeriya da jinya ta yi ajalinsu
Tun yana ƙarami, mahaifinsa Ardo Adamu ya rasu, abin da ya sa ya taso cikin maraici. Amma kasancewarsa na 23 a jerin ’ya’yan mahaifinsa, ya sa ya samu damar rayuwa cikin dangi gaba da baya.
Shi ne mutum na biyu a duka faɗin Najeriya da ya rike shugabancin ƙasar nan a zamanin mulkin Soja da kuma farar hula.
Rayuwarsa ta soja
Ya shiga aikin soja a shekarar 1961, inda ya taka muhimmiyar rawa a yaƙin basasar da aka yi tsakanin 1967 zuwa 1970.
Ya riƙe muƙamin Gwamnan tsohuwar Jihar Borno na watanni uku, a zamanin mulkin soja na Murtala Ramat Muhammad.
Daga 1976 zuwa 1978, lokacin mulkin soja na Olusegun Obasanjo, ya riƙe muƙamin Ministan Albarkatun Man Fetur.
Marigayi Muhammadu Buhari, da gungun wasu sojoji sun jagoranci juyin mulki da ya kawar da gwamnatin farar hula ta Shehu Usman Shagari, inda ya hau mulki daga watan Disambar 1983 zuwa Agustan 1985.
Gwamnatinsa ta soji, ta yi yaƙi da rashin ɗa’a, da cin hanci da rashawa.
Ganin yadda aka shaidi gaskiyarsa, ya sa daga baya gwamnatin tsohon shugaban ƙasa na mulkin soji, Janar Sani Abacha, ta ba shi jagorancin asusun tattara rarar man fetur tare da sarrafa su, wato PTF.
A lokacin, Buhari ya nuna ba sani ba sabo, wajen tattalin kuɗin, tare da yin amfani da su wajen inganta ilimi, samar da magunguna, gina tituna da dai sauransu.
Dawowar mulkin Dimokuraɗiyya
Shekaru huɗu da dawowar dimokuraɗiyya, Jamhuriya ta Huɗu, ’yan siyasa suka jawo Muhammadu Buhari cikin harkokin siyasa, inda ya fara fitowa takarar shugabancin ƙasa a 2003 a inuwar Jam’iyyar APP, sai kuma 2007 a ANPP, inda duka ya ƙarƙare a mataki na biyu.
A zaɓen 2011, ya kafa sabuwar jam’iyya tasa wato CPC, inda a nan ne farin jininsa ya ƙara fitowa fili, ganin yadda yazo na biyu a zaɓen shugaban ƙasa, duk da rashin daɗewar jam’iyyarsa.
Bayan dunƙulewar jam’iyyun adawa na ANPP, CPC da ACN, da wasu gwamnonin jam’iyyar PDP mai mulki, zuwa tafiyar haɗaka ta APC, a 2015 Muhammadu Buhari ya sake fitowa takara.
A zaɓen fitar da gwanin Jam’iyyar APC ya doke Rabi’u Musa Kwankwaso da Atiku Abubakar, kafin daga bisani ya lashe zaɓen shugaban kasa.
Zaɓen ya zo da ba zata, inda karon farko shugaban ƙasa mai ci, ya fadi zaɓe.
Shugaban ƙasar lokacin, Goodluck Jonathan, da kansa ya kira Buhari a waya, ya taya shi murna.
Marigayi Muhammadu Buhari, ya shafe shekara takwas yana mulki a wa’adi biyu daga 2015 zuwa 2023.
Gwamnatinsa ta fuskanci ƙalubalen rashin tsaro da hauhawar farashin abinci da sauran kayan masarufi.
A gefe guda, gwamnatinsa ta fito da tsare-tsaren taimakon manoma na cikin gida, musamman manoman shinkafa, domin ganin ’yan Najeriya sun riƙa noma abincin da za su ci.
Ta kuma bijiro da hanyoyi daban-daban na tallafa wa ’yan ƙasa, mata da matasa, kamar shirin N-Power, tallafin ƙananan ’yan kasuwa na Trader Money, Survival Fund, Bankin NIRSAL da sauransu, waɗanda ba a taɓa ganin irinsu ba a baya.
Haka kuma shi ne shugaban da ya sanya hannu a kan Dokar Man Fetur, wadda aka shafe shekaru 20 ana kai-komo a ƙudurin, musamman kan sarƙaƙiyar da ke tattare da biyan tallafin mai.
Kazalika a lokacin shugancinsa aka fara haƙo ɗanyen mai a Arewa a Arewacin Najeriya a yankin Kolmani da ke tsakanin jihar Gombe da Bauchi.
A fannin tsaro kuma an yi nasarar ceto da dama daga cikin dalilan makarantar Chibok da Dapchi da ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP suka yi garkuwa da su.
A gefe guda kuma gwamnatinsa ta bijiro da wasu tsare-tsare masu cike da ruɗani kamar tsarin taƙaita amfani da tsabar kuɗi, da rufe iyakokin Najeriya domin ƙarƙafa noma a cikin gida.
Yunƙurin assassawa da kuma farfaɗo da wasu muhimman ayyuka kamar gina layin jirgin ƙasa daga Arewacin Najeriya zuwa Jamhuriyar Nijar da gyaran titin Abuja zuwa Kaduna sun fuskanci suka kan tafiyar hawainiyarsu.
Haka kuma zargin cin hanci ya dabaibaye jami’an gwamnatinsa, musamman kan aikin tashar wutar lantarki ta Mambilla da dambarwar kafa kamfanin jiragen sama na Nigeria Air a ƙarshen mulkinsa da sauransu.
Haka kuma an zargi gwamnatin tasa da rauni wajen ɗaukar matakan yaƙar cin hanci da kuma magance matsalar tsaro da ta garkuwa da mutane da suka yi ƙamari musamman a yankin Arewa.
Dame za a ke tuna shi
Za a rika tuna Marigayi Muhammadu Buhari, a matsayin mutum mai gaskiya, da kaffa-kaffa da dukiyar al’umma.
Sannan yana ɗaya daga cikin mutane ƙalilan da suka fi kowa riƙe muƙamai a tarihin Najeriya, amma ba tare da an tuhume shi da almundahana ba.
Ya rasu yana da shekara 83 a duniya.
Ya shafe rayuwarsa da mata biyu, Safinatu Yusuf da ya yi rayuwar mulkin soja da ita. Sai A’isha Halliru, wadda aka fi sani da Aisha Buhari da ya yi rayuwar farar hula da ita.
Ya rasu ya bar ’ya’ya takwas da jikoki da dama.