✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Katsina ta ba da hutun jimamin rasuwar Buhari

Rasuwar Buhari ta girgiza dan uwansa Malam Mamman Daura, sai da aka garzaya da shi asibiti

Gwamnatin Jihar Katsina ta ayyana Litinin din nan a matsayin ranar hutu don jimamin rashin tsohon shugaban kaas Muhammadu Buhari.

Sanarwar hakan nda Sakataren Gwamnatin Jihar, Barrista Abdullahi Garba Faskari, ya fitar da yammacin ranar Lahadi, ta bayyana cewa hutun zai bai wa ma’aikatan jihar damar ta’aziyyar wannan babban rashi da aka yi.

Sanarwar ta ƙara da cewa gwamnan, Malam Umaru Dikko Radda, ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga iyalai da al’mmar jihar kan wannan gagarumin rashi.

Ya bayyana Shugaba Buhari a matsayin mai kishin ƙasa da son cigaban talaka, wanda ya gudanar da rayuwarsa wajen hidima wa ƙasar sa da jiharsa.

Ya yi roƙon Allah Ya gatarfa masa kuma ya bai wa iyalinsa haƙurin wannan rashi.

Ana sa ran nan gaba za a gudanar da jana’izar tsohon shugaban kasan a mahaifarsa da ke Daura a Jihar ta Katsina.

Buhari ya kasance shugaban kasar a Najeriya sau biyu, inda ya yi shugaban kasa na mulkin soji a matsayin shugaban kasa na bakwai.

Daga baya ya yi mulkin shekara hudu a karkashin tsarin dimokuradiyya daga shekarar 2015 zuwa 2023, a matsayin shugaba na 15.

Ya rasu yana da shekaru 83 a yayin da yake jinya a wani asibiti da ke birnin Landan a kasar Birtaniya, shekara biyu bayan saukarsa daga karagar mulki.

Rahotanni sun bayyana cewa labarin rasuwar Buhari ta girgiza kawunsa kuma na hannun damansa, Malam Mamman Daura, sai da aka garzaya da shi asibiti. Zuwa wannan lokaci dai ba mu da cikakken bayani game da halin da Mamamn Daura ke ciki.

Tuni shugabanni da attajirari masu fada a ji da daidaikun jama’a suka yi ta mika sakonnin ta’aziyyarsu game da wannan rashi, suna addu’ar rahama da Buhari tare da bayyana kyawawan halayensa.