Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta dakatar da zamanta na tsawon sati biyu domin juyayin rasuwar tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari.
Akawun Majalisar, Kamoru Ogunlana, ya sanar a safiyar Litinin cewa Majalisar ta ɗage zamantafa kwana 12, har zuwa ranar 22 ga watan nan na Yuli, 2025.
Sanarwar ta bayyana, “Ana kiran daukacin mambobin Majalisar Dokoki ta Tarayya su sauya ayyukansu na majalisa zuwa ranar Talata 22 ga watan Yuli 2025 domin su samu damar halartar ta’azaiyyar.”
Ya kara da mika ta’aziyya ga al’umma da gwamnatin Jihar Katsina da ma Najeriya game da wannan rashi.