Jama’a da dama sun yi jimami tare da ta’aziyyar rasuwar Tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, wanda ya rasu a wani asibiti da ke Birnin Landan, bayan gajeriyar rashin lafiya.
Buhari, ya rasu yana da shekaru 83 a duniya, ya rasu ya bar mata ɗaya da ’ya’ya da kuma jikoki da dama.
- Tsoffin zaɓaɓɓun shugabannin Najeriya da jinya ta yi ajalinsu
- Tinubu ya tura Shettima Landan domin ɗauko gawar Buhari
Bola Tinubu
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana mutuwar Buhari a matsayin babban rashi ga Najeriya.
A cikin sanarwar da ya fitar, Shugaba Tinubu, ya bayyana Buhari a matsayin gwarzo, soja, kuma shugaban da ya sadaukar da rayuwarsa wajen gina haɗin kan ƙasa.
“Buhari ya kasance gwarzon ɗan ƙasa da ya shugabanci Najeriya da cikakkiyar sadaukarwa. Daga mulkin soja a shekarar 1984 zuwa shugabancin dimokuraɗiyya daga 2015 zuwa 2023, ya tabbatar da kishin ƙasa da gaskiya,” in ji Shugaba Tinubu.
Atiku Abubakar
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana mutuwar Buhari a matsayin babban rashi da zai bar giɓi a tarihin ƙasar nan.
“Buhari bai kasance shugaban ƙasa kawai ba, ya kasance abin kafa misali wajen ɗa’a, ƙwazo, da son ƙasa. Rayuwarsa ta kasance darasi ga kowane ɗan Najeriya,” in ji Atiku.
Peter Obi
Shi ma Peter Obi, ya bayyana Buhari a matsayin shugaba mai mutunci, wanda ya yi shugabanci da ƙima da ƙwazo.
Ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan Buhari, musamman Hajiya Aisha Buhari da ’ya’yansa, tare da yin addu’ar Allah Ya jikansa da rahama.
“Ya Ubangiji, ka gafarta masa, ka karɓe shi cikin rahamarka, ka sanya shi cikin Aljannah Firdausi,” in ji Obi.
Olusegun Obasanjo
Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya ce Buhari ya rasu a lokaci da Najeriya ta fi buƙatar gogewar tsofaffin shugabanni domin fuskantar matsalolin da ke addabar ƙasar.
“Buhari ya taka rawar gani a matsayinsa na soja, shugaba, kuma dattijo. Mutuwarsa rashi ne da yi wa ƙasar nan giɓi,” a cewarsa.
Rabiu Musa Kwankwaso
Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana alhininsa na rasu Muhammadu Buhari.
“Ina miƙa ta’aziyyata ga iyalansa da kuma Gwamnatin Jihar Katsina da kuma Najeriya baki ɗaya.
“Ina addu’ar Allah Ya jiƙansa da rahama.”
Shugaban Majalisar Wakilai, Abba Tajudeen
Shugaban Majalisar Wakilai, Abbas Tajudeen, ya bayyana Buhari a matsayin ɗaya daga cikin ’yan Najeriya mafi kishin ƙasa da suka rayu. Ya ce rayuwarsa ta kasance abun koyi, cike da gaskiya da kawaici, kuma yana daga cikin shugabannin da suka tsaya tsayin daka wajen yaƙar rashawa.
“Ya rasu bayan ya yi shekaru 83, inda ya sadaukar da mafi yawan rayuwarsa wajen yi wa Najeriya hidima. Tare da Tinubu da wasu, ya taimaka wajen kafa jam’iyyar APC wadda ta ƙwace mulki daga hannun PDP a 2015,” in ji Abbas.
Gwamnatin Katsina
Gwamnatin Jihar Katsina da Masarautar Katsina, sun bayyana jimaminsu bisa rashin ɗa a gare su.
Hakazalika, manyan ’yan siyasa daga Arewa da sauran sassan Najeriya, sun bayyana alhini tare da miƙa ta’aziyya ga al’umma baki ɗaya.
A yayin da Najeriya ke jimamin wannan babban rashi, an tabbatar da cewa za a shirya jana’izar Buhari a Daura kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, inda an kawo da gawarsa daga Landan.