Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya dawo gida Najeriya bayan kwashe makonni biyu, inda ya ziyarci ƙasashen Saint Lucia da Brazil.
Mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga, ne ya sanar da hakan a shafinsa na X.
Shugaba Tinubu ya bar Najeriya ne a ranar 28 ga watan Yuni, 2025 don ziyarar aiki a waɗannan ƙasashe biyu.
Da farko ya je Saint Lucia domin ƙarfafa dangantaka tsakanin Najeriya da ƙasashen yankin Caribbean, da kuma ƙara haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen kudancin duniya.
A ranar 4 ga watan Yuli, Tinubu ya tashi daga Saint Lucia zuwa Brazil, inda ya halarci taron BRICS na shekarar 2025, wanda aka gudanar daga 6 zuwa 7 ga watan Yuli, 2025.