✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya kamata mulkin Najeriya ya ci gaba da zama a hannun ’yan Kudu — Hannatu Musawa

Ministar ta ce ya kamata mulkin ya kasance a hannun Kudancin Najeriya domin samun daidaito.

Ministar Raya Al’adu, Hannatu Musawa, ta ce ya kamata shugabancin ƙasar nan ya ci gaba da kasancewa a hannun ’yan Kudu domin a samu adalci da daidaito.

Ko da yake kundin tsarin mulkin Najeriya bai tilasta tsarin karɓa-karɓa ba, manyan jam’iyyun siyasa suna bin tsarin sauya mulki tsakanin Arewa da Kudu.

A wata hira da ta yi da gidan talabijin na Channels a ranar Juma’a, Hannatu Musawa ta ce tun da an samu Shugaba daga Arewa (Muhammadu Buhari) na tsawon shekaru takwas, to ya dace yanzu kuma a bar ’yan Kudu su yi shekaru takwas.

A shekarar 2023 ne Bola Ahmed Tinubu, wanda ɗan Kudu ne, ya gaji Buhari daga Arewa bayan kammala wa’adin mulkinsa.

Ministar ta ce: “Bayan shekara takwas na mulkin Buhari daga Arewa, ya kamata yanzu ’yan Kudu su ma su samu damar yin shekaru takwas don a samu adalci.”

A kwanakin baya, tsohon gwamnan Benuwe, Samuel Ortom, ya bayyana cewa ba zai goyi bayan ɗan takara daga Arewa ba.

Maganar karɓa-karɓa tsakanin Arewa da Kudu wani batu ne da ake ta muhawara a kai a siyasar Najeriya, kuma wasu masana na ganin yana hana dimokuraɗiyya ci gaba yadda ya kamata.