✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An gabatar da Ganduje a matsayin shugaban kwamitin hukumar FAAN

Keyamo ya ce yana da yaƙinin za su aikin cikin ƙwarewa don samar da ci gaba.

An gabatar da Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Abdullahi Ganduje, a matsayin Shugaban Kwamitin Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta Ƙasa (FAAN).

Wannan naɗin ya biyo bayan murabus ɗin da Ganduje ya yi daga shugabancin APC kwanan nan, inda ya bayyana cewa ya yi hakan saboda wasu muhimman dalilai na ƙashin kansa.

Jam’iyyar ta maye gurbinsa da Ali Bukar Dalori a matsayin shugaban riƙon ƙwarya.

Gbenga Saka, mai bai wa Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, shawara kan harkokin dijital, ya wallafa bidiyon bikin rantsar da Ganduje a shafin X.

Ganduje, wanda tsohon Gwamnan Jihar Kano ne, ya kasance cikin kwamitin hukumar tare da wasu kamar su: Ms Olubunmi Kuku, Babbar Daraktar FAAN, Ms Dorothy Duruaka, Ahmed Ibrahim Suleiman.

Sauran sun haɗa da Nasiru Muazu, Omozojie Okoboh, TP Vembe da kuma Bridget Gold a matsayin sakatariyar kwamitin.

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ne, ya naɗa Ganduje shugaban wannan kwamitin tun a watan Janairun 2025.

A wajen bikin, Minista Festus Keyamo ya ce: “Muna sa ran wannan kwamitin zai taimaka wajen bunƙasa harkokin sufurin jiragen sama a ƙasar nan, haɗa yankuna daban-daban, da kuma kawo ci gaban tattalin arziƙi.

“Duk da ƙalubale kamar matsalar gine-gine da sauye-sauyen da ke faruwa a harkar jiragen sama a duniya.

“Ina da tabbacin ƙwarewarku za ta taimaka wajen cimma burin FAAN.”