Aminu Dahiru Ahmad, hadimin tsohon shugaban jam’iyar APC na kasa, Abudllahi Umar Ganduje, ya ce jam’iyyar za ta gane ta yi kuskure kan saukarsa daga shugabancin.
A wata doguwar wasika da ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya bayyana takaicinsa kan rashin nuna wa Ganduje halasci, duk da irin ci gaban da ya kawo jam’iyar wanda ya ce ba a taba samun makamancinsa ba.
“Tarihin APC ba zai manta da Ganduje ba — Shi ya kai ta matsayin da take kai yanzu,” inji shi.
- Gwamnatin Tinubu na shirya mana zagon ƙasa — ADC
- An ƙayyade maki da shekarun shiga jami’a a Nijeriya
Aminu ya ba da misali da yadda aka dinga tururuwar shiga APC a lokacin mulkin Ganduje da kuma yadda Gwamnoni suka dinga sauya sheka, wanda ya ce ko hakan ya isa ya nuna kwarewarsa a fagen siyasa.
“A lokacinsa ne karon farko da wata jam’iyyar siyasa a Najeriya ta ga cancantar samar da wata dama da nufin magance matsalar shigar matasa a harkokin siyasa.”
A wani sakon da ya wallafa kafin wasikar, ya ce za su rama biki idan lokaci ya yi, kuma a nan ne za a gane Ganduje shi ne rufin asirin APC.
“Tinubu ya mana rauni sau daya, sau biyu, har sau uku. Allah Ya kai mu ranar ramuwa, ranar da za su gane cewa shi ne rufin asirinsu,” in ji shi.
A bayan nan ne dai tsohon gwamnan na Kano, Ganduje ya ajiye muƙaminsa na shugabancin jam’iyyar APC.
Duk da yake Ganduje ya ce rashin lafiya ce ta sa ya yi murabus, wasu majiyoyi sun bayyana cewa rikicin siyasa a cikin jam’iyyar ne suka tilasta masa ajiye muƙamisa.
Ganduje ya zama Shugaban APC a watan Agustan 2023, a lokacin da jam’iyyar ke fama da rikicin cikin gida.