Jam’iyyar ADC ta zargin Fadar Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinuba da shirya mana wata kutungwila mai hadarin gaske domin kawo cikas ga hadakar ’yan adawan da ke kara samun farin jini.
Sakataren Yada Labarai na ADC na Kasa, Malam Bolaji Abdullahi, ya ce a sakamakon haka gwamnatin APC a matakin kasa ta kira wani taron sirri tsakanin wasu manyan jami’an gwamnati da shugabbanin jam’iyyar ADC na jihohi da kuma kusoshinta daga yankin Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas.
Ya ci gaba da cewa, hadafin taron na su shi ne “kawo rudani a jam’iyyarmu, bayyana shugabanninta a matsayin haramtattu da kum kawar da ita daga manufofin da ta sanya a gaba, lura da karuwar yadda jam’iyyar take kara samun farin jini a tsakanin ’yan Najeriya
“Daga haka ake fara samun kasa mai tsarin jam’iyya daya—ta hanyar barazaa,” in ji jami’in na ADC.
“Amma kuma a maimakon ta gyara kurakurenta sai ta kare da kokarin amfani da tsohuwar dabararta ta kawo rudani a jam’iyyun adawa.”