✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu ko ɗansa zai naɗa shugaban INEC, APC sai ta faɗi zaɓen 2027 — Dalung

Tsohon ministan ya ce APC wata mafaka ce ta gurɓattun 'yan siyasa.

Tsohon Ministan Matasa da Wasanni, Solomon Dalung, ya ce duk wani yunƙuri da Shugaba Bola Tinubu, zai yi ba zai hana jam’iyyar APC faɗuwa a zaɓen 2027 ba.

Yayin wata hira da aka yi da shi a Jos, a Jihar Filato, Dalung, ya ce ko da Tinubu zai naɗa ɗansa Shugaban Hukumar Zaɓe (INEC), ko matarsa ta zama Babbar Alƙalin Alƙalai ta Ƙasa, hakan ba zai taimaka wa APC ba.

Ya ce gwamnatin APC ta gaza, kuma ta jefa ‘yan Najeriya cikin ƙunci da yunwa ta hanyar manufofinta marasa kan gado.

Dalung ya ce: “Ko duk gwamnonin jihohi 36 za su koma APC, kuma Tinubu ya naɗa ɗansa shugaban INEC, sai sun faɗi a 2027. Wannan karon tsakanin talakawa da gwamnati ne.”

Ya ƙara da cewa ‘yan Najeriya su shirya wa zaɓen 2027 domin ƙalubalantar gwamnatin Tinubu wadda ta jefa su cikin yunwa, talauci, da rashin adalci.

Dalung, ya bayyana jam’iyyar APC a matsayin mafakar muggan ‘yan siyasa, inda ya ce jam’iyyar ba ta da tsari ko aƙida, kuma yawaitar masu sauya sheƙa zuwa cikinta zai haddasa mata rikici nan ba da daɗewa ba.

Ya bayyana dalilin ficewarsa daga APC zuwa jam’iyyar SDP, inda ya ce taron da suka yi da Tinubu ya ba shi kunya, domin shugaban bai fahimci matsalolin da suka tattauna ba.

Dalung, ya kuma soki shugabannin siyasar Najeriya gaba ɗaya, inda ya bayyana cewa suna tafiyar da ƙasar ne ta hanyar son kai.