✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan Majalisar Wakilai bakwai na Akwa Ibom sun koma APC

Cikin waɗanda suka sauya sheƙa sun haɗa da shida daga Jam’iyyar PDP da kuma ɗaya daga Jam’iyyar YPP.

A ci gaba da sauya sheƙar da ’yan Majalisar Wakilai na Tarayya ke yi a ranar Alhamis wasu mambobi bakwai daga Jihar Akwa Ibom sun sanar da sauya sheƙa zuwa Jam’iyyar APC mai mulki.

Cikin waɗanda suka sauya sheƙa sun haɗa da shida daga Jam’iyyar PDP da kuma ɗaya daga Jam’iyyar YPP.

Shugaban Majalisar Wakilan Tarayya Tajudeen Abbas ne ya karanta wasiƙunsu na sauya sheƙa a zauren Majalisar a ranar Alhamis yayin zaman majalisar.

’Yan majalisar dai sun yi nuni da ƙara samun rarrabuwar kawuna da rigingimun cikin gida a cikin Jam’iyyar PDP a matsayin dalilin da ya sa suka yanke shawarar ficewa daga jam’iyyar.

Waɗanda suka sauya sheƙa daga PDP sun haɗa da: Paul Ekpo da Unyime Idem da Martins Etim da Okpolu Ukpong Etteh da Uduak Odudoh da Okon Ime Bassey.

Shi ma ɗan Majalisa Emmanuel Ukpong-Udo na Jam’iyyar YPP ya koma APC.

’Yan majalisar dai sun ce rikicin da ya ɓarke a Jam’iyyar PDP a Akwa Ibom da ma ƙasa baki ɗaya ya sa ba su iya wakiltar mazaɓarsu yadda ya kamata.

Ficewar ta zo ne makonni kaɗan bayan gwamnan Jihar Akwa Ibom, Umo Eno ya koma APC.

Da yake mayar da martani game da sauya sheƙar, shugaban marasa rinjaye na majalisar, Kingsley Chinda ya nuna baƙin cikinsa game da ci gaban da aka samu.

Chinda ya ce, iƙirarin rarrabuwar kawuna a cikin Jam’iyyar PDP bai dace ba kuma ya saɓawa doka.