Babbar jam’iyyar hamayya a Nijeriya, PDP ta ce za ta ɗauki tsattsauran mataki kan mambobinta da ke ƙoƙarin shiga sabuwar haɗakar ƙawancen jam’iyyun hamayya ta ADC.
Yayin da yake jawabi ga manema labarai bayan taron kwamitin amintattun jam’iyyar, shugaban jam’iyyar na ƙasa Ambasada Iliya Damagum ya ce jam’iyyar tana gargaɗi ’yan’yanta da ke shirin shiga sabuwar haɗakar ADC.
Damagum ya ce ƙoƙarin da haɗakar ke shirin yi ba zai yi tasiri ba, yana mai cewa da dama daga cikin mambobin haɗakar za su koma jam’iyyunsu.
“Yana da kyau su sani cewa babu inda ya kamata a haɗu domin tunkarar gwamnatin APC da ya wuce jam’iyyar PDP, amma in suna ganin ba haka ba, to su je su gwada su gani, amma dai na san dole za su dawo”, in ji shi.
Shugaban riƙon ya kuma gargaɗi ’yan PDP da ya ce suna ƙoƙarin “sayar da jam’iyyar”.
Kawo yanzu dai akwai jiga-jigan PDP cikin sabuwar haɗakar ta ADC, ciki har da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a zaɓen da ya gabata, Atiku Abubakar.
A farkon makon nan ne dai jam’iyyar PDP ta gudanar da taronta na Kwamitin Zartaswa da a ciki ta ce ta ɗinke ɓarakar da ta ɗauki tsawon lokacin tana fama da ita a cikin jam’iyyar.
Mun shirya fito-na-fito da APC — Malami
Shi ma dai tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami wanda a yau Laraba ya sanar da ficewa daga jamiyyar APC, ya ce a shirye haɗakar ADC take wajen yaƙi da gwamnatin APC domin kawo “gyara kan yadda ake tafiyar da gwamnati.”
Malami —wanda ya kasance minista a zamanin gwamnatin tsohon shugaban Nijeriya, Mumammadu Buhari — ya ce ukuɓar da gwamnati Tinubu ta sanya talakawan Nijerya a ciki ba za ta misaltu ba.
A hirarsa da BBC, Abubakar Malami ya ce sun fito fili ne domin su yaƙi jam’iyyar APC mai mulki, musamman yadda ta bar abubuwa da dama sun tabarbare a ƙasar, ciki har da tsaro da tattalin arziki da kuma sauran dangogin wahalhalu da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta jefa talakawa.
“A duk lokacin da wata tarayya ta zo da wasu tsare-tsare na ƙuntata wa al’umma, da sanya su cikin halin wahala to wajibi a taru wuri guda su dauki mataki domin kawo sauyi ta hanyar maido da kaykkyawan tsari, da zai ɗaɗa wa mutane”, in ji shi.
“Mun yanke hukuncin ɗaukar mataki domin yaƙi da rashin tsaro da ynuwa domin maido da Nijeriya kan turba mai kyau da tsari”, in ji Malami.
David Mark ya zama shugaban ADC na kasa
Tuni dai haɗakar hammayar ADC ta tabbatar da naɗin tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata David Mark a matsayin sabon shugabanta na ƙasa.
Sanata David Mark, ya bayyana cewa ƙawancen ADC, haɗaka ce da ta shafe watanni ana tattaunawa domin samar da ita.
Ya ambato manyan matslolin tsaron da ke addabar jahohin Kaduna da Katsina da Zamfara da Sokoto da Borno da Yobe da sauran su, da cewa duk wani da ya damu da halin da ake ciki mai alaƙa da hakan, ya amince da shiga wannan haɗaka tasu.
Ya ce duk waɗanda suka hallara a taron da zuciya ɗaya suka amince da ɗunkewar.
David Mark ya kuma ce daga cikin fatansu shi ne ceto Nijeriya da kuma al’ummar kasar.
A taron haɗakar na jiya ne aka tabbatar da naɗin tsohon gwamnan Jihar Osun, Rauf Aregbesola a matsayin sakataren jam’iyyar na ƙasa.