Jam’iyyar PDP a Jihar Kebbi, ta bayyana shirinta na haɗa kai da sauran jam’iyyu da ƙungiyoyi domin karɓe mulki daga hannun APC a zaɓen 2027, a matakin jiha da kuma tarayya.
An bayyana wannan matsaya ne a garin Birnin Kebbi ranar Asabar, yayin wani taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar, inda aka jaddada buƙatar yin sulhu da warware rikicin cikin gida da ke damun PDP.
- Mutanen Sakkwato na neman ɗaukin gwamnati game da Bello Turji
- An samu amincewar yi wa Dantata jana’iza a Madina
Jigo a jam’iyyar, Ibrahim Mera, ya ce sun amince su haɗa kai da kowa domin a samu nasarar kawar da APC a jihar.
“Za mu yi aiki tuƙuru don ganin haɗakar ta yi tasiri. Mun amince a shirya zaɓen shugabanni a duk lokacin aka ba da izini daga matakin ƙasa,” in ji shi.
Shugaban PDP a Jihar Kebbi, Usman Suru, ya nemi afuwar jama’a bisa halin matsin da suke ciki, ya kuma ce akwai fatan samun sauyi mai amfani a gaba.
Shi ma tsohon ɗan takarar gwamna na PDP a zaɓen 2023, Janar Aminu Bande (mai ritaya), ya soki matsin tattalin arziƙi da halin da jihar ke ciki, inda ya zargi gwamnatin APC da tsare ‘yan adawa ba bisa ƙa’ida ba.
“Zan mara wa PDP baya a duk wani yunƙurin da za ta yi domin a kawo gwamnati mai adalci a Kebbi da Najeriya gaba ɗaya,” in ji shi.
Jam’iyyar PDP ta ce tana da yaƙinin cewa da haɗin kai da gyaran cikin gida, za ta iya samun nasara a 2027.