Shugaban Najeriya, Bola Tinubu na ziyarar aiki a cikin Jihar Kaduna.
Shugaba Tinubu na ziyarar ne domin ƙaddamar da wasu ayyuka da gwamnan jihar, Uba Sani ya aiwatar a tsawon shekara biyu da ya yi yana mulkin jihar.
- Za a dawo da dukkan Alhazai gida ranar 28 ga Yuni – NAHCON
- Kotu ta ba da belin Natasha kan N50m kan zargin bata sunan Akpabio
Wasu daga cikin ayyukan da shugaban ya ƙaddamar sun haɗa da: asibitin ƙwararru mai gadaje 300 da gwamnatin jihar ta gina don bunƙasa harkokin lafiya.
Daga nan kuma shugaban ya ƙaddamar da cibiyar koyar da sana’o’i, da kuma motocin sufuri masu amfani da iskar gas ta CNG guda 100.
A cikin waɗanda suka yi wa Shugaba Tinubu rakiya sun haɗa da: Mataikamin Shugaban ƙasa na musamman kan harkokin siyasa, Sanata Ibrahim Masara, da mai taimaka wa shugaban kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu da Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Barau I. Jibrin da wasu manyan jami’an gwamnati.