Kungiyoyin ma’aikata na Kwalejin Ilimi ta jihar Kaduna da ke Gidan Waya, Kafanchan sun bayyana aniyarsu na fara yajin aikin gargadi na kwanaki uku.
Sun ce za su shiga yajin aikin ne daga ranar Alhamis, 19 ga watan Yuni, 2025.
Wannan matakin ya biyo bayan karewar wa’adin kwanaki 14 da suka yi bai wa gwamnatin jihar, wanda zai kare ranar Laraba, 18 ga watan Yuni.
- Majalisa ta aike wa Tinubu kudurorin dokar haraji domin ya rattaba musu hannu
- Ambaliyar Mokwa: Har yanzu muna neman mutum 700 – Gwamnatin Neja
Aminiya ta rawaito cewa kungiyoyin da suka hada da na Kungiyar Malaman Kwalejojin Ilimi (COEASU), SSUCOEN da Kungiyar Manyan Ma’aikatan Kwalejojin Ilimi ta Najeriya (SSUCOEN) da Kungiyar Ma’aikatan da ba na Koyarwa ba (NASU), na bukatar daukar matakin gaggawa kan batutuwan walwalar ma’aikata da suka ce gwamnati ta yi sakaci da su duk da alkawuran da ta riga ta daukar musu.
Sanarwar ta fito ne daga wani taron manema labarai da Shugaban Hadaddiyar Majalisar Ma’aikatan, Kwamared Alkali Marajos ya jagoranta.
Daga cikin manyan bukatun da kungiyoyin ke nema akwai aiwatar da tsarin albashi na CONPCASS da CONTISS da kuma gyara dokar ritaya ta shekaru 65 don ta shafi hatta ma’aikatan da ba masu koyarwa ba.
Kungiyoyin sun gargadi cewa rashin cika wadannan bukatu zai tilasta musu fara yajin aikin gargadi daga 19 zuwa 23 ga Yuni, 2025.
Sai dai sun sake jaddada aniyarsu ta ci gaba da tattaunawa tare da bukatar gwamnatin jihar da ta dauki matakin gaggawa domin kaucewa tsaiko ga harkokin karatu a makarantar.