✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An tallafa wa mata 250 da abinci da kayan sana’a a Kaduna

'Yar kasuwar ta ce za ta ci gaba da raba irin wannan tallafi ga mabuƙata.

Wata ’yar kasuwa mai taimakon al’umma, Barista Catherine Bitrus, ta raba wa mata 250 da abinci da kayan sana’a a garin Manchok da ke Ƙaramar Hukumar Kaura, a Jihar Kaduna.

Tallafin ya haɗa da injinan niƙa, buhunan shinkafa, katan-katan na taliyar yara, da man girki.

A lokacin rabon kayan, Catherine, shugabar kamfanin Natural Beauty Secret, ta ce ta yi hakan ne domin taimaka wa matan karkara da ke fama da matsaloli a rayuwa.

“Allah Ya ba ni arziƙi, shi ya sa na ga dacewa na raba da waɗanda ke bukata,” in ji ta.

“Na zaɓi mata ne domin na san irin wahalar da suke sha.”

Ta roƙi matan da su dage da ƙoƙari, ka da su yanke ƙauna, domin komai na duniya yana da mafita idan aka jajirce.

Catherine ta ce tana da niyyar ci gaba da wannan aiki, kuma ta yaba wa Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, saboda irin goyon bayan da yake bai wa mata a jihar.

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na jihar, Barista James Kanyip, ya yaba da wannan aiki, inda ya buƙaci sauran masu hali da ƙungiyoyin su dinga tallafa wa marasa ƙarfi.

Shugaban kwamitin shirya taron, Lucky Ezra, ya bayyana Catherine a matsayin mace mai zuciyar taimako da kishin jama’a.

A madadin sauran matan da suka amfana, Josephine Bature ta nuna farin ciki da godiya, tare da addu’ar Allah Ya saka wa Catherine da alheri.