Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta mata ta Najeriya, Super Falcons, ta sake kafa tarihi bayan ta doke ƙasar Maroko da ci 3–2 a wasan ƙarshe na gasar WAFCON.
Yanzu haka Super Falcons ta lashe kofin karo na 10, wanda shi ne adadi mafi yawa da wata ƙasa ta taɓa lashewa a tarihin gasar.
- ADC ce kaɗai za ta iya magance matsalolin Arewa — David Mark
- Dole gyaran kundin tsarin mulki ya haɗa kan ƙasa da shugabanci na gari — Abba
Maroko ce ta fara jefa ƙwallaye biyu cikin mintuna 25 ta hannun Ghizlane Chebbak da Sanaa Mssoudy, lamarin da ya tayar da hankalin magoya bayan Super Falcons a filin wasa na Rabat.
Amma Najeriya ba ta karaya ba.
A minti na 64, Esther Okoronkwo ta warware ƙwallo a bugun fenariti, sannan ta taimaka wajen cin ƙwallo ta biyu da Folashade Ijamilusi ta jefa a minti na 71.
Saura minti biyu a tashin daga wasan, Jennifer Echegini ta ci ƙwallo ta uku, wanda hakan ya sa ta girgiza duniyar ƙwallo.
Wannan nasara ta tabbatar da mamayar da Super Falcons ta yi a Afirka.
Ƙungiyar ta lashe dukkanin wasanim ƙarshe da ta buga a gasar WAFCON, kuma yanzu tana da kofuna 10 a tarihin gasar.