Majalisar Dinkin Duniya ta nada Farfesa Rabi’a Sa’id, daga Jami’ar Bayero ta Kano (BUK), a wani sabon kwamitin bincike kan illar amfani da makaman nukiliya.
Farfesa Rabi’a Sa’id nanada masaniyar kimiyyar nukiliya ce kuma kwararriya a fannin kimiyyar yanayi, wadda ta jaddada mahimmancin samun wakilcin Afirka a tattaunawar da suka shafi tsaron duniya da rayuwar bil’adama.
Wannan kwamitin, wanda aka kafa a karkashin kudurin Majalisar Dinkin Duniya na 79/238, zai tantance tasirin amfani da makaman nukiliya zai haifar ga muhalli da lafiya da kuma tattalin arzikin.
Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres, ya zabi Farfesa Sa’id daga cikin kwararru 21 na duniya don shiga kwamitin, wanda aka dora wa alhakin gabatar da cikakken rahoton kimiyya nan da shekarar 2027.
- Muna samun sauki bayan hatsarin mota — Gwamna Radda
- NAJERIYA A YAU: Abin da ya sa muke yi wa PDP zagon ƙasa —Sule Lamiɗo
- Gwamnan Katsina ya tsallake rijiya da baya a hatsarin mota a hanyar Daura
Aikin masaniyar zai fi mayar da hankali kan kimanta sauye-sauyen yanayi bayan yakin nukiliya da kuma tasirin zafinsa, don tabbatar da cewa an hada da ra’ayoyin Afirka da Najeriya.
Wannan nadin ana ganin sa a matsayin wata babbar nasara ga rawar da Najeriya ke takawa a fannin zaman lafiya, kula da lafiya, da tsaron duniya.
Kazalika ana kallon sa a matsayin wani babban ci-gaba ta fannin diflomasiyar kimiyya, musamman ga mata a fannin kimiyya, fasaha, injiniyanci da lissafi (STEM) a duk fadin Afirka.