Aƙalla mutum 14; ciki har da mata da ƙananan yara ƙanana ne, suka rasu a wani sabon hari da aka kai a Jihar Filato.
Harin ya faru ne da yammacin ranar Alhamis a Gundumar Mangor da ke Ƙaramar Hukumar Bokkos.
Waɗanda aka kashe suna kan hanyarsu ta dawowa daga kasuwar mako-mako da ke garin Bokkos, lokacin da wasu ’yan bindiga suka buɗe musu wuta.
Wannan hari na zuwa ne wata guda bayan wani hari da aka kai wa wasu ‘yan ɗaurin aure daga Zariya a Jihar Filato, inda aka kashe su.
Ƙungiyar Bokkos Cultural Development Forum (BCDF), ta tabbatar da faruwar harin.
Shugaban ƙungiyar, Farmasum Fuddang, ya ce suna jimami da ɓacin rai saboda wannan hari, musamman ganin cewa an sha gudanar da zaman sulhu tsakanin manoma da makiyaya.
Ya ƙara da cewa mata da ƙananan yara na daga cikin waɗanda suka rasu.
Fuddang, ya danganta harin da wata ƙabila.
Ya kuma ce wata ƙungiyar ta’addanci tana ƙone ƙauyuka da ƙwace gonaki a yankin Mushere.
A cewarsa, burinsu shi ne su mamaye dukkanin Ƙaramar Hukumar Bokkos, wadda ta ke hedikwatar noman dankalin turawa a Najeriya.
Sai dai makiyaya a yankin sun ce ba su da hannu a cikin harin.
Shugaban Gan Allah Fulani Development Association (GAFDAN) na yankin, Saleh Adamu, ya karyata zargin, inda ya bayyana cewa babu wata shaida da ke nuna cewa Fulani ne suka kai harin.
Ya ce ba a kama ko mutum ɗaya daga cikin makiyaya a wajen da harin ya auku ba, kuma ya ce wannan zargi sabon abu ne da bai taɓa faruwa a yankin ba.
Saleh ya ƙara da cewa, “A duk lokacin da wani abu ya faru, jami’an tsaro su kan gudanar da bincike kafin a gano waɗanda suka aikata laifin. Muna Allah-wadai da wannan hari baki ɗaya.
“Kisan mutane marasa laifi ba shi da wani uzuri da za a aminta da shi.”
A halin yanzu, jami’an tsaro ba su fitar da wata sanarwa dangane da harin ba.
Wakilinmu ya tuntuɓi jami’an hulɗa da jama’a na Operation Safe Haven, Manjo Samson Zhakom, da na rundunar ’yan sandan jihar, DSP Alabo Alfred, amma ba su ce komai ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.